Sarkin Sasa ya nemi a yi wa Najeriya da Buhari addu’a
Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a jihohi 17 na Kudancin Najeriya, Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa Malam Haruna Maiyasin ya yi kira ga ’yan Najeriya su rika yi wa kasar haihuwarsu addu’ar zama lafiya a kowane lokaci. Ya ce ya lura cewa akwai mutane masu yawa da suke yin sako-sako da yi irin wadannan addu’o’i, a maimakon […]
Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a jihohi 17 na Kudancin Najeriya, Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa Malam Haruna Maiyasin ya yi kira ga ’yan Najeriya su rika yi wa kasar haihuwarsu addu’ar zama lafiya a kowane lokaci. Ya ce ya lura cewa akwai mutane masu yawa da suke yin sako-sako da yi irin wadannan addu’o’i, a maimakon haka sai masu hannu da shuni daga cikinsu suka dukufa wajen yin amfani da dukiyarsu domin tayar da zaune tsaye a cikin kasa.
Malamin ya fadi haka ne cikin hira da Aminiya a fadarsa da ke Sasa a birnin Ibadan. Ya tunatar da al’ummar Najeriya, Musulmi da Kirista a game da muhimmancin girmama shugabanni da yi masu addu’a. Ya nuna rashin jin dadinsa a kan kalaman batanci da wasu mutane suke yi wa Shugaba Muhammadu Buhari. Ya ce addinin Musulunci bai amince da yin kazafi da zagi da raina shugaban al’umma ba, domin yin haka yana iya haifar da masifu iri-iri da tabarbarewar al’amuran mulki da zai iya
jefa jama’a cikin kuncin rayuwa da damuwa.
“Ina yin kira ga ’yan Najeriya su ci gaba da rokon Allah Ya kara wa Shugaba Buhari lafiya kuma ya yi masa jagoranci da zai iya sauke nauyin da yake kansa. Muna mika godiyarmu ga Allah madaukaki da ya amsa addu’o’in da miliyoyin jama’a na ciki da wajen Najeriya suka yi a lokacin da Shugaba Buhari yake jinya a kasar Ingila. Wannan alama ce da ke nuna muhimmancin rokon Allah da zuciya daya domin neman biyan bukatar abun alheri, domin shi ne (Allah) Ya ce a nemi biyan bukata daga gare shi, domin shi kadai ne mai bayarwa. Kuma wannan wata hikima ce ta Ubangiji da ya nuna wa masu mummunar fata cewa ba su isa ba,” inji Sarkin Sasa.
Da yake amsa wata tambaya, ya jinjina wa Shugaba Buhari ne a kan salon shugabanci da yin siyasa ba da gaba ba da yake yi a halin yanzu, a inda ya fara nuna haka a lokacin da ya gayyaci gwamnonin jihohi 36 na kasa ya zauna tare da su domin tattaunawa a kan yadda za a yi maganin matsalolin da suka shafi kasa baki daya. Ya ce ya kamata wadannan gwamnoni su jingine mummunar siyasa waje daya, su mara wa shugaban baya domin samun nasarar gudanar da muhimman ayyukan ci gaba da jama’ar kasa za su amfana.
Ya yi kira ga dukkan ’yan Arewacin kasa da ke zaune a wannan sashe, su girmama shugabanninsu kuma su kyautata zamantakewarsu da jama’ar garuruwan da suke zaune.