Sarkin Sasa ya yi bikin cika shekara 31 a karaga
Shugaban majalisar sarakunan Hausawa a jihohi 17 na kudancin kasa, Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin, ya yi bikin cikarsa shekara 31 a kan karagar mulki a harabar fadarsa dake garin Sasa, a Ibadan a ranar Asabar da ta wuce.A hirarsa da wakilinmu, Sarkin na Sasa, ya nuna farin cikinsa na cika shekaru 31 […]
Shugaban majalisar sarakunan Hausawa a jihohi 17 na kudancin kasa, Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin, ya yi bikin cikarsa shekara 31 a kan karagar mulki a harabar fadarsa dake garin Sasa, a Ibadan a ranar Asabar da ta wuce.
A hirarsa da wakilinmu, Sarkin na Sasa, ya nuna farin cikinsa na cika shekaru 31 a karaga, bikin da aka gudanar, inda ya mika godiya ga Allah (SWT) da ya ba shi damar yi wa jama’a aiki tsakani da Allah na tsawon wannan lokaci. Sannan ya jinjina wa sarakunan Hausawa da suka ba shi hadin kai da goyon baya da ya kai shi ga samun nasarar hada kawunan sarakunan , domin tafiya da murya guda, sabanin yadda ta kasance a baya.
Ya ce, babbar matsalar da ya fuskanta a cikin shekaru 31 da yayi bisa karaga, ita ce, “yunkurin da wasu miyagun mutane a tsakaninmu suka yi wajen karkatar da ni daga ayyukan hada kan jama’a da ci gabansu, tare da yin adalci a tsakaninsu, ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba. Wannan shi ne kalubalen da na fuskanta amma, Allah bai ba su sa’a ba. Babu wanda ya isa ya kawar da akalar gaskiya da adalci da nake rungume da ita, domin kowa ya aikata laifi ko ‘ya’ya na ne, to kuwa zan kalle su da irin laifin da suka aikata ne.
“ Na ki jinin barawo da masu cin dukiyar jama’a su ki biya da gangan da masu kulle-kullen makirci, domin tayar da husuma a cikin jama’a,” inji shi.
Da yake amsa wata tambaya, Alhaji Haruna Maiyasin, a cewarsa : “Ni ban taba rike mutum a zuciya ta ba, kuma ba na yin gaba da kowa sai dai su yi gaba da ni, wanda ni ban san abin da suke yi ba, domin a boye suke yin abubuwan na su.”
Sarkin na Sasa, ya yi amfani da wannan dama wajen nada wasu manyan mutane sarautun gargajiya. Gwamnonin jihohin Kano da Sakkwato da Osun da tsohon Gwamnan jihar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim, suna daga cikin wadanda aka ba su sarautun, ta hannun wakilansu. Shi kuwa Shugaban kungiyar mutanen wasu jihohi da ke zaune a Jihar Oyo, Sir, (Cif) Michael U. Orji da ya samu sarautar dan Jikan Jihar Yamma, ya jagoranci daruruwan manbobin kungiyar ne domin taya shi murna.
Sarkin Noma, Alhaji Garba Ba’are, wanda likkafa tayi gaba zuwa Magajin Garin Sasa, ya ce: “Kowa ya sani cewa, Mai martaba Sarkin Sasa, ya samu kyakkyawar shaidar hidimta wa Najeriya ta fannoni daban-daban, musamman hada kawunan al’umma da samar da zama lafiya da ya cancanci gwamnatin kasar nan ta girmama shi da lambar yabo.” Shi ma Tafidan Ibadan, Alhaji Hassan Isyaka, wanda ya samu sarautar Sarkin Kudun Jihar Yamma, ya nemi al’ummar Arewacin kasa da ke zaune a sashen Kudu ne, su mara wa Sarkin Sasa baya da kyawawan shawarwari da za su taimaka wajen cimma buri.
Sarakuna da malaman addinai da ‘yan siyasa da shugabannin kungiyoyin kabilu daga sassa daban-daban na kasar nan ne suka halarci wannan biki, inda jami’an tsaro suka cika aikinsu wajen tabbatar da ganin an gudanar da bikin lami lafiya. Su ma masu kade-kade da bushe-bushe da raye-raye sun burge dimbin mahalarta bikin da irin al’adunsu.
Ya ce, majalisarsa ta dakatar da taron da ta saba yi a tsakanin sarakunan Hausawan Kudu ne saboda kada a kalle su da wata manufa daban da ci gaban jama’arsu. ‘A maimakon haka sai muka raba zaman namu zuwa shiyya-shiyya da kowace shiyya za ta kawo sakamakon abubuwan da ta tattauna zuwa wajen babban taro da za mu yi a nan gaba.
“Ka san al’amarin siyasar kasar nan babu gaskiya, ga ita kanta gwamnati saboda haka idan muna yawan yin taro, sai su ga kamar muna son tona musu asiri ne, ko kuma wata kiyayya muke son kawo musu,” inji shi.