Sarkin Saudiyya ya bukaci a fito addu’ar rokon ruwa
Shugaban masu hidimta wa Masallatai biyu mafi alfarma na Makkah da Madina, Sarki Salman bn Abdulaziz na kasar Saudiyya, ya kirayi jama’ar kasar da su fito sallar rokon ruwan a ranar Alhamis mai zuwa. Sanarwar hakan ta fito ne ranar Litinin daga fadar Masarautar Kasar Saudiyya kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ya wallafa. […]
Shugaban masu hidimta wa Masallatai biyu mafi alfarma na Makkah da Madina, Sarki Salman bn Abdulaziz na kasar Saudiyya, ya kirayi jama’ar kasar da su fito sallar rokon ruwan a ranar Alhamis mai zuwa.
Sanarwar hakan ta fito ne ranar Litinin daga fadar Masarautar Kasar Saudiyya kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ya wallafa.
- Saudiyya za ta koma aiki da motoci masu amfani da lantarki
- An kama sigarin Dala 10m da aka yi fasakwauri a China
- Masu halin bera sun hana ruwa gudu a gwamnatin Buhari — Ndume
Sanarwar ta ce, addu’ar rokon ruwan sama abu ne mai kyau da ya zo daidai da koyarwar Annabi Muhammad (S.A.W.).
Sarki Salman ya kira da daukacin al’umar kasar da su gudanar da Addu’o’i da neman yafiyar Ubangiji da mika wuya a garesa tare da yi wa juna afuwa domin samun rabauta da Rahama.
A bisa al’ada a kan gudanar da sallar rokon ruwan sama wadda a harshen larabci ake kira Isitisqa yayin da aka samu fari ko kuma neman tsagaitawar ruwa a lokacin da ya yi yawan gaske.