Sarkin Tanagle ya kai karar talakawansa kotu
Mai Tangale Malam Abdu Buba Maisheru II ya yi karar wadansu mutum 28 da suka fito daga masarautarsa a gaban Kotun Majistare da ke garin billiri bisa zarginsu da laifuffukan hadin baki da razanarwa da cin zarafi da zagi da kuma tayar da tarzoma a tsakanin jama’a a ranar Lahadi 5 ga Yunin bana da […]
Mai Tangale Malam Abdu Buba Maisheru II ya yi karar wadansu mutum 28 da suka fito daga masarautarsa a gaban Kotun Majistare da ke garin billiri bisa zarginsu da laifuffukan hadin baki da razanarwa da cin zarafi da zagi da kuma tayar da tarzoma a tsakanin jama’a a ranar Lahadi 5 ga Yunin bana da misalin karfe 7:00 na dare.
Mutanen da Sarkin yake kara sun hada da Luka Ibrahim da Solomon Samuel da Yayirus Yusuf da Isa’ac Ibrahim da Irimiya Daniel da Ali T. Yaro da Gideon danladi da Deborah Daniel da Patricia danladi da Ordeji Waziri, dukkansu suna zaune ne a Unguwar Poshiya a karamar Hukumar billiri ta Jihar Gombe, inda Sarkin yake zargin sun hada baki da wadansu mutum 18 da suka hada da Kefas Dable da Daniel Stephen da Matan Mela da Mery Garba da Moses Kanti da Philibus Panso da Mela Lakasdi da Gayus danladi da Rose Daniel da Ezikiel Daniel da Tangani Laualbani da Mary Maikai da Yar Lawjiton da Maina Mato da Lachirai Samuel da Hajiya Zainab Garba wadanda suka gudu, wajen aikata laifuffukan da ake zargi.
Ana zargin mutanen da hada baki su je Fadar Mai martaba Mai Tangale Abdu Buba Maisheru II inda suka tsare shi suka razanar da shi suka jefe shi da duwatsu wanda yin hakan ya jawo rashin zaman lafiya a yankin.
dan sanda mai gabatar da kara Kufur Kelbin Modu ya bayyana wa kotun cewa aikata hakan laifi ne day a saba wa sassa na 97 da 397 da 155 da kuma 114 na kundin laifuffuka da hukuncinsu na Final Kod.
Da kotun ta juya ga wadanda ake tuhumar sun musanta laifin da ake zarginsu da aikatawa, inda dan sanda mai gabatar da karar ya shaida wa kotu cewa akwai sauran mutum 18 da ba su shiga hannu ba, amma ’yan sanda sun dukufa wajen nemo su.
Daga bisani dan sandan ya karo mutum uku da suka hada da Kefas Dable da Mary Garba da Philibus Pano.
Wadanda aka gurfanar a gaban kotun dan sandan ya nemi kotun ne ta gargade su kan su zama masu hali nagari, kuma sun rubuta takardar yarjejeniyar ba za su sake aikata wani laifi makamancin haka ba, inda ya kuma shaida wa kotun cewa an janye karar wadanda ake tuhumar da suka halarci kotun, amma wadanda suka gudu shari’arsu tana nan a gaban kotun idan suka shiga hannu.
Alkalin kotun Mai shari’a Muhammad Jungudo, ya amince da yarjejeniyar janye karar.