Sarkin Tikau a Yobe ya riga mu gidan gaskiya
Za a rika tunawa da Mai Tikau bisa karamcinsa, da kaunar talakawa.
Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Tikau, Alhaji Muhammadu Abubakar Ibn Grema rasuwa a ranar Juma’a.
Rasuwar sarkin mai daraja ta ɗaya ta jefa al’ummar Sabon Garin Nangere da ke Karamar Hukumar Nangere cikin ruɗani kamar yadda wakilinmu ya ruwaito.
- Abin da ke ƙara ta’azzara adawa tsakanin Davido da Wizkid
- An kashe makiyaya 2 da shanu 150 a sabon hari a Filato
Wata majiya da ke kusa da fadar Tikau ta ce, Sarkin ya rasu ne a Asibitin Kwararru na garin Potiskum bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Majiyar ta ce sai nan gaba kadan za a sanar da cikakkun bayanai game da jana’izar marigayi sarkin na Tikau.
“Za a rika tunawa da Mai Tikau bisa karamcinsa, da kaunar talakawa, da kuma gwarzon kare muhalli tare da kula da harkokin addini,” kamar yadda wani mai rike da sarautar gargajiya a masarautar, Honarabul Abdulrahman Nangere ya bayyana wa Aminiya.
Masarautar Tikau ita ce daya tilo a Jihar Yobe wadda ake alakanta ta da masarautar ’yan kabilar kare-kare duk da cewar masarautar ta Tikau ta kunshi har da kabilun Fulani, Ngizim da sauransu.