Sarkin yaƙin masarautar Zazzau ya rasu ana tsaka da taro
An yi jana’izar mamacin da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Alhamis.
Masarautar Zazzau ta sanar da rasuwar ɗaya daga cikin manyan fadawan Sarkin Zazzau, kuma Sarkin Yaƙin Zazzau, Alhaji Rilwanu Yahaya Pate, da safiyar ranar Alhamis yayin da ake tsaka da taro a Babban Asibitin Gambo Sawaba da ke Kofar Gayan, Zariya.
Marigayin yana cikin tawagar Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, lokacin da mutuwa ta riske a wajen taron da kwamitin abokai na asibitin ya shirya.
- Ɓarayin dabobbi sun shiga hannu, an ƙwato awaki 85 a Gombe
- Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai
Da yammacin ranar Alhamis, aka yi jana’izarsa a gidansa da ke Rimin Doko, a Unguwar Kaura, a cikin Birnin Zariya.
Babban Limamin Zazzau, Malam Dalhatu Kasim Imam ne, ya jagoranci sallar jana’izar da aka yi da misalin ƙarfe 5 na yamma.
Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, tsofaffin gwamnonin Jihar Kaduna, Alhaji Ahmad Makarfi da Alhaji Muktar Ramadan Yero, da kuma sauran al’umma ne suka halarci jana’izar.
A saƙon ta’aziyyarsa, Sarkin Zazzau ya jajanta wa iyalan mamacin da ɗaukacin masarautar bisa wannan babban rashi.
Ya kuma roƙi Allah Ya gafarta wa mamacin tare da bai wa iyalansa haƙurin jure rashinsa.