Sarkin Yakin Bauchi: Hakimin da ya fi tsufa a Masarautar Bauchi ya kwanta dama

Al’ummar Masarautar Bauchi da na Jihar Bauchi sun shiga da alhini da jimamin rasuwar Sarkin Yakin Bauchi kuma hakimin da ya fi kowane hakimi tsufa a masarautar Alhaji Muhammadu Usmanu Maidawa. Marigayin ya rasu yana da shekara 118 a duniya An haifi marigayi Sarkin Yakin Bauchi Alhaji Muhammadu Maidawa ne  a 1901 kuma ya rasu […]

Sarkin Yakin Bauchi: Hakimin da ya fi tsufa a Masarautar Bauchi ya kwanta dama

Marigayi Sarkin Yaqin Bauchi Alhaji Muhammadu Usmanu Maidawa yana miqa sanda ga Sarkin Bauchi

Al’ummar Masarautar Bauchi da na Jihar Bauchi sun shiga da alhini da jimamin rasuwar Sarkin Yakin Bauchi kuma hakimin da ya fi kowane hakimi tsufa a masarautar Alhaji Muhammadu Usmanu Maidawa.

Marigayin ya rasu yana da shekara 118 a duniya

An haifi marigayi Sarkin Yakin Bauchi Alhaji Muhammadu Maidawa ne  a 1901 kuma ya rasu ranar Juma’ar da ta gabata 1 ga Faburairun nan, daidai yana da shekara 118 a duniya.

Marigayi Sarkin Yaki Muhammadu Maidawa ya yi aiki a matsayin magatakardan kotu inda ya shekara 35 yana aikin har zuwa lokacin da ya yi ritaya kafin ya shiga harkokin sarauta.

An nada shi Sarkin Kudun Bauchi Hakimin Kasar Lame a   1976 wanda Kakan Sarkin Bauchi na yanzu marigayi Sarkin Bauchi Malam Adamu Jumba ya nada shi. Kuma saboda amanarsa sai marigayi Sarkin Bauchi Alhaji  Dokta Sulaiman Adamu Jumba. ya nada shi a Sarautar Sarkin Yakin Bauchi Hakimin Kasar Lame a 1994, shekara 25 da suka gabata.

Nada shi wannan  sarauta ya sanya shi kasancewa daya daga cikin mutum shida da ke zaben Sarki a Masarautar Bauchi, Kuma shi ma Babbban Kansila ne ko dan Majalisar Sarkin Bauchi. Sannan shi ne mutum na biyu a jerin manyan hakimai daga gaba in Sarki ya yi hawa bayan tawagar Madakin Bauchi sai tawagar Sarkin Yakin Bauchi.

Ya rasu ya bar matan aure biyu da ’ya’ya 14. Daga cikin ’ya’yansa akwai babban dansa Alhaji Korau, sai Garba Mohammed ’Yandoton Bauchi. Akwai Rufa’i Mohammed, akwai kuma Yakubu Mohammed, Yeriman Wunti da Dan Madamin Wunti Bello Mohammed  akwai ’yarsa wadda ta auri marigay Sarkin Lere  da ke Jihar Kaduna Alhaji Umaru Mohammed.

Marigayi Sarkin Yakin Bauchi shi ne mutum na 18 da ya yi wannan sarauta. Sarkin Yaki na farko shi Malam Muhammadu Kusu daga 1812-1820, sai Jibir daga 1822-1842,  sai Abdulkadir Muhammadu Kusu daga 1842-1855 sai Usman Hardo Sambo daga 1855-1857, sai Ahmadu Muhammadu Kusu daga 1857-1896, sai Iya Jibir daga1895 -1897 da Muhammadu Ahmadu daga 1897 -1901 da Umaru Alkamu daga 1905-1907 sai Ali Ahmadu daga 1908-1909, sai Hassan Bello Usman daga 1909-1924, sai Abubakar Ibrahim daga 1924-1929 sai, Usmanu Bello daga 1929-1938, sai Usman Babale daga 1938-1965, sai Alhaji Yakubu Abubakar OFR daga 1965-1993 sai kuma shi marigayi Muhammadu Usmanu Maidawa  daga 1994-019. Wannan sarauta ta Sarkin Yaki gidaje biyu ne ke neman sarautarta daga gidan Muhammadu Kusu marigayi Sarkin Yakin Bauchi na farko da kuma gidan Jibir dukan wadanda suka yi sarautar jinin wadannan bayin Allah ne. Al’ummar Jihar Bauchi sun bayyana rasuwar marigayi Sarkin Yakin a matsayin babban rashi wanda ya bar gibi mai wuyar cikewa.

Alhaji Muhammadu Bashari (Mai Daura) wanda dan marigayi Sarkin Yaki Yakubu Abubakar ne da Alhaji Muhammadu Bello sun ce rasuwar Sarkin Yakin babban rashi ne ba ga masarautar Bauchi kadai ba har ma ga Daular Usmaniyya da Najeriya baki daya. “Mun rasa uba adali mutumin da ba ya son zalunci, mai tsoron Allah mutumin kirki, mai tawali’u da tawakkali. Mun rasa  mutum marar tsoro mai gaskiya mai son fadin gaskiya wanda ko wane ne ya aikata rashin gaskiya Sarkin Yaki zai je kansa kai-tsaye ya fada masa ba tare da shakka ko tsoro ba, kuma mutum ne mai son zaman lafiya ba ya son tashin hankali. Uba ne da bai yarda da wargi ba kuma yanayin komai cikin tsari. Allah Ya jikansa Allah Ya gafarta masa,” inji su.