Sarkin Yawuri ya nada uban kasar Giron-Masa da Zaruman Yawuri

Mai martaba Sarkin Yawuri Alhaji Zayyanu Abdullahi ya nada Alhaji Shehu Ahmad Sawa Uban kasar Giron-Masa da Umaru Ahmadu Gado a matsayin Zaruman Yawuri, a wani biki da ya samu halartar fitattun mutane da suka fito daga sassan Najeriya. A jawabinsa bayan kammala nadin, Alhaji ZayyanuAbdullahi ya ce, ya nada Alhaji Shehu Ahmad Sawa, Uban […]

Sarkin Yawuri ya nada uban kasar Giron-Masa da Zaruman Yawuri
Sarkin Yawuri ya nada uban kasar Giron-Masa da Zaruman Yawuri

Mai martaba Sarkin Yawuri Alhaji Zayyanu Abdullahi ya nada Alhaji Shehu Ahmad Sawa Uban kasar Giron-Masa da Umaru Ahmadu Gado a matsayin Zaruman Yawuri, a wani biki da ya samu halartar fitattun mutane da suka fito daga sassan Najeriya. A jawabinsa bayan kammala nadin, Alhaji ZayyanuAbdullahi ya ce, ya nada Alhaji Shehu Ahmad Sawa, Uban kasar Giron -Masa ne saboda irin dimbin gudunmawar da yake bayarwa ga ci gaban masarautar da yadda yake sa hannu a duk wani al’amari da ya shafi al’ummar Yawuri, inda ya yi fatar sabon uban kasar zai ci gaba da nuna kishin da yake yi da tallafa wa al’umma domin ci gaban masarautar Yawuri da Jihar Kebbi da Najeriya baki daya. Alhaji Shehu Sawa ya gode wa Sarkin Yawuri da ’yan majalisarsa kan goyon bayan da suka ba shi, domin ba shi kadai ya nemi sarautar ba, amma Allah Ya zabe shi sannan kuma da goyon bayan Sarkin da ’yan majalisarsa. Ya ce shi da Zarumai da aka ba wannan sarautu da yardar Allah ba za su ba Sarki da ’yan majalisarsa kunya ba.