Sarkin Zamfara Ya bukaci gwamnonin kasar nan su ba Gwamna Yari goyon baya

Mai martaba Sarkin Zamfaran Anka kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, Alhaji Attahiru Ahmad Muhammad ya bukaci gwamnonin kasar nan su bai wa sabon shugaban kungiyar Gwamnoni ta Najeiriya kuma Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar goyon bayan don ya samu nasarar jagorantar kungiyar zuwa ga samun nasara. Sarki Attahiru Ahmad ya yi wannan […]

Sarkin Zamfara Ya bukaci gwamnonin kasar nan su ba Gwamna Yari goyon baya
Sarkin Zamfara Ya bukaci gwamnonin kasar nan su ba Gwamna Yari goyon baya

Mai martaba Sarkin Zamfaran Anka kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, Alhaji Attahiru Ahmad Muhammad ya bukaci gwamnonin kasar nan su bai wa sabon shugaban kungiyar Gwamnoni ta Najeiriya kuma Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar goyon bayan don ya samu nasarar jagorantar kungiyar zuwa ga samun nasara.

Sarki Attahiru Ahmad ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a fadarsa da ke Anka, inda ya ce kungiyar ta gwamnoni ba ta yi zaben tumun-dare
ba, domin ta zabi wanda ya dace, kuma gwarzon dan siyasa da ya san hakkin al’umma.
Sarkin ya ja hankalin gwamnonin su maida hankali wajen samar wa matasa aikin yi a kasar nan, musamman ta hanyar maida hankali wajen inganta noma da hakar ma’adinai ta ingantacciyar hanya.
Ya ce a karamar Hukumar Anka kawai akwai wajen hakar ma’adinai har 45, ban da wadanda suke wasu kananan hukumomi da ke jihar.
Sarkin ya kara da cewa a inganta harkar noma domin shi ne mutanen kasar nan suka fi sani, sai kasuwanci wanda da shi ne suka budi ido, ya ce hakan zai taimaka wajen rage zaman kashe wando da kuma yawaitar batagari a tsakanin jama’a.
Sarkin ya ce su a Jihar Zamfara suna fama da barayin shanu da suke zuwa da miyagun makamai su kwashe dabbobin mutane su kuma kashe su har su yi wa matansu fyade.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi su taimaka a kara inganta jami’an tsaro da kayan aiki, inda ya kawo misali cewa akwai wani ofishin ’yan sanda da ke masarautarsa da suka ce a yanzu bindigogi uku kawai suke da su, don haka babu yadda za a yi su tunkari masu dauke da miyagun makamai masu yawa.
Ya ce ya wajaba a taimaka wa ’yan sanda, saboda su ma mutane ne, ya ce akan samu kowa yana barci amma suna gadin jama’a da dukiyarsu, amma duk da haka wasu na yi musu kallon banza. Ya cewa idan dan sanda ya mutu kafin hakkinsa ya fito sai an manta da shi iyalansa sun tagayyara, inda ya ba da misali da wani dan sanda da ya mutu a masarautarsa amma sai da suka hada kudi aka kai shi garinsu domin bisne shi.