Sarkin Zango ya nemi ’yan Arewa a Kudu su gyara halayyarsu

Sarkin Zango Benin, Alhaji Muhammed Jingudo ya yi kira tare da neman ’yan Arewa mazauna Kudu su kasance masu da’a su gyara halayyarsu da dabi’unsu domin samun maido da martaba da darajarsu, musamman mazauna Jihar Edo da ma Kudu baki daya. Alhaji Muhammadu Jingudo ya yi wannan bayanin ne tare da yin kira ga ’yan […]

Sarkin Zango ya nemi ’yan Arewa a Kudu su gyara halayyarsu

Sarkin Zango Benin, Alhaji Muhammed JingudoSarkin Zango Benin, Alhaji Muhammed Jingudo ya yi kira tare da neman ’yan Arewa mazauna Kudu su kasance masu da’a su gyara halayyarsu da dabi’unsu domin samun maido da martaba da darajarsu, musamman mazauna Jihar Edo da ma Kudu baki daya.
Alhaji Muhammadu Jingudo ya yi wannan bayanin ne tare da yin kira ga ’yan Arewa a cikin wata zantawar da ya yi da wakilin Aminiya a garin Benin, inda ya bayyana matukar damuwa tare da takaici game da abin da ya kira bata-gari da suke aikata barna ta hanyoyi daban-daban cikin birnin Benin da kauyuka. “Abin bakin ciki ne rahotannin muke samu suna bayyana a ciki irin yawan ayyukan barna da wasu matasa ’yan Arewa suke aikatawa, lamarin da ya sa ake yi wa duk wanda ya fito daga yankin Arewa kallon-kallo.
“Saboda haka nake kira ga ’yan Arewa mazauna Jihar Edo da sauran na yankin Kudu baki daya su baiwa shugabanni goyon baya tare da hadin kai domin yakar irin wadannan masu  miyagun dabi’u ’yan bara-gurbi ta hanyar fallasa su ga hukumomi, don a samu damar kakkabe su cikin jama’a. Yin haka zai kawo zaman lafiya ya wanzu tare da samun ci gaba tare da maido da martabar ’yan Arewa a nan Kudu da kasa baki daya”. Inji shi.
Daga nan sai ya yi kira ga hukumar ’yan sanda ta jihar ta taimaka wajen kakkabe irin wadannan bata-gari da suka addabi jama’a. “Ina kara kira ga Mista Folusho Ayodeji Adebanjo, kwamishinan ’yan sanda na jihar ta Edo da ya ci gaba da kokarin da yake yi domin tabbatar da jihar ta samu kyakkyawar makoma a bangaren tsaro ta hanyar kakkabe irin wadanda suka maida wasu unguwanni a cikin garin Benin dabar aikata ayyukan assha”. Inji shi.