Sarkin Zazzau ya bukaci a rika gina masallatai da makarantu
Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya bukaci al’ummar Musulmi, musamman masu kudi da su rika gina masallatai da makarantu domin daukaka Musulunci.Sarkin ya yi wannan kira ne a lokacin da yake bude sabon masallacin da aka gina a harabar Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna a ranar Talatar da ta gabata.Ya kara da cewa, […]
Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya bukaci al’ummar Musulmi, musamman masu kudi da su rika gina masallatai da makarantu domin daukaka Musulunci.
Sarkin ya yi wannan kira ne a lokacin da yake bude sabon masallacin da aka gina a harabar Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna a ranar Talatar da ta gabata.
Ya kara da cewa, ko shakka babu akwai lada da amfanu ga duk wanda ya daure ya gina masallaci da makaranta domin daukaka kalmar Allah. Don haka sai ya yaba wa hukumar ta Alhazan, musamman shugabanta Alhaji Kabir Kasim a bisa wannan namijin kokari da ya yi na gina sabon masallacin.
A jawabinsa, shugaban hukumar, ya bayyana cewa an gina masallacin ne da taimakon wasu bayin Allah masu hannu da shuni. Ya ce masallacin zai dauki akalla masallata sama da 200 a lokaci guda, sannan an gina shi ne saboda maye gurbin tsohon masallacin da ke harabar, wanda ke daukar masallata arbain kacal.
Sabon masallacin dai an kawata shi ne irin na zamani kuma akwai sashen mata daban.