Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Sarkin ya buƙaci sabbin hakiman da su kasance masu riƙon amana da gaskiya a tsakanin al’ummarsu.

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya naɗa sabbin hakimai guda bakwai domin tallafawa al’amuran masarautar.

An gudanar da bikin naɗin ne a fadar Sarkin Zazzau da ke Zariya, inda jama’a daga sassa daban-daban suka halarta.

Sarkin, ya ce an zaɓo sabbin hakiman ne bisa tarihinsu da kuma irin gudunmawar da suka bayar ga masarautar a Jihar Kaduna, da kuma Najeriya baki ɗaya.

Da yake magana ta bakin babban mashawarcinsa, Alhaji Abas Ahmed Fatika, Sarkin ya buƙaci sabbin hakiman da su yi amfani da ƙwarewarsu wajen ciyar da masarautar gaba tare da kawo ci gaba a al’amuran da suka shafi al’adun masarautar.

Har ila yau, ya yi kira da su inganta haɗin kai, zaman lafiya, da juriya a tsakanin al’ummarsu, tare da bayar da gudunmawa wajen zamantakewa, tattalin arziƙi da ilimi.

Sarkin, ya gargaɗe su da guje wa duk wani abu da zai saɓa wa al’adun al’umma, tare da tunatar da su cewar suna wakiltar masarautar ne a duk inda suka samu kansu.

Sabbin hakiman da aka naɗa sun haɗa da: Dan Isa; Alhaji Mustapha Aliyu Shehu Idris, Sarkin Dawakin Tsakar Gida; Alhaji Junaid Muhammadu, Ciroman Dawaki; Alhaji Musa Tijjani Umar.

Sauran sun haɗa da Janjuna; Alhaji Suleiman Mijinyawa, Daneji; Alhaji Salisu Hamza, Tafidan Kudu; Alhaji Lawal Mukhtar Sambo, Tafidan Arewa; Alhaji Abdullahi Yahaya Makama.

’Yan Bindiga: An miƙa wa gwamnatin Kaduna mutum 58 da aka ceto

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna

Barikin Ladi: Asalin garin da yanayin rayuwar mazauna