Sarkin Zazzau ya nada hakimai 8

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ne ya rantsar da sabbin hakiman a fadarsa da ke birnin Zariya.

Sarkin Zazzau ya nada hakimai 8

Sarkin Zazzau yana mika wa daya daga cikin Hakiman masarautar takwas da ya nada. (Hoto: Twitter/DZubairu daga
Nata’ala Emirates).

Masarautar Zazzau ta nada karin sabbin hakimai takwas tare da mika musu takardun fara aiki.

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ne ya kaddamar da sabbin hakiman a wani kwarya-kwaryan biki a fadarsa da ke birnin Zariya.

Sarkin Zazzau ya kuma mika wa sabbin hakiman takardunsu na aiki, wanda ya nuna nadin nasu sun fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Fabrairu, 2023.

An nada su ne bayan amincewar Gwmanan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta hannun Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu ta jihar.

Sabbin Hakiman su ne:

  1. Alhaji Sufiyanu Umar Usman, Karfen Dawakin Zazza, Hakiman Pambegua.
  2. Mohammed Dahiru Dikko, Barde Kankanan Zazzau – Hakimim Pala.
  3. Haruna Abubakar Bamalli, Barde Kerrariyyan Zazzau – Hakimin Zangon Aya.
  4. Alhaji Kabiru Zubairu, Madaucin Arewan Zazzau – Hakimim Barnawa
  5. Dokta Bello Lawal, Durumin Zazzau – Hakimim Gubuchi respectively.
  6. Abdulkarim Zailani – Hakimim Sabon Birni
  7. Alhaji Auwalu Aliyu Damau – Hakimim Samu
  8. Alhaji Aminu Mohammed Ashiru – HakiminHunkuyi.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos