Sarkozy zai fuskanci shari’a a Faransa

Wani babban alkali a kasar Faransa ya ba da umarnin a gurfanar da tsohon Shugaban kasar, Nicolas Sarkozy kan badakalar kudaden yakin neman zabensa a shekarar 2012. Ana zargin Sarkozy da jam’iyyarsa ta UMP da boye wasu kudaden yakin neman zabensa da suka kai Yuro miliyan 18. Amma tsohon Shugaban Faransar ya musanta zargin inda […]

Sarkozy zai fuskanci shari’a a Faransa

Wani babban alkali a kasar Faransa ya ba da umarnin a gurfanar da tsohon Shugaban kasar, Nicolas Sarkozy kan badakalar kudaden yakin neman zabensa a shekarar 2012.

Ana zargin Sarkozy da jam’iyyarsa ta UMP da boye wasu kudaden yakin neman zabensa da suka kai Yuro miliyan 18.

Amma tsohon Shugaban Faransar ya musanta zargin inda ya ce ba ya da masaniya game da kashe kudaden da suka zarce adadin da aka ware domin yakin neman zaben..

Lauyan da ke kare Sarkozy, Thierry Herzog ya ce za su daukaka kara domin kalubalantar matakin na kotun.

Sarkozy dai ya sha kaye a zaben shekarar 2012 wanda aka Francois Hollande ya lashe.

Dokokin Faransa sun sanya iyaka kan yawan kudaden da za a iya kashewa yayin yakin neman zabe. Sai dai bayanai sun ce Jami`yyar UMP ta Sarkozy ta kashe kudaden da suka zarce adadi ta hanyar kawance da wani kamfani da ake kira Bygmalion.

Haka kuma rahotanni suna nuna cewa ana zargin Mista Sarkozy da karbar makudan kudi daga marigayi Shugaban Libya Muhammar Ghadafi domin yakin zabensa.