Sarrafa Albarkatun Gona: Citta
A wannan makon zan fara bayanin yadda dan kasuwa zai sarrafa citta a matsayin daya daga cikin albarkatun gona da ake samu a kasar nan domin sayarwa a kasuwannin cikin gida da na kasashen ketare. Ita dai citta saiwa ce ta wata shuka da ake nomanta a jihohin tsakiyar Najeriya, musamman ma jihohin Kaduna da Gombe […]
A wannan makon zan fara bayanin yadda dan kasuwa zai sarrafa citta a matsayin daya daga cikin albarkatun gona da ake samu a kasar nan domin sayarwa a kasuwannin cikin gida da na kasashen ketare.
Ita dai citta saiwa ce ta wata shuka da ake nomanta a jihohin tsakiyar Najeriya, musamman ma jihohin Kaduna da Gombe da Bauchi da Binuwai da Nasarawa. Nigeriya ce kasa ta shida wajen noman citta a duniya, inda ake samun kimanin tan dubu 160; kuma ita ce kasa ta uku a duniya wajen fitar da citta a kasuwannin duniya, bayan kasar Sin (China) da kasar Indiya.
Ana amfani da citta ta fannoni da dama a kusan dukkanin sassan duniya. Citta sinadari ce a abincin al’umma da yawa a kasashen duniya, inda wadansu ke amfani da ita domin inganta dandanon abinci ko inganta kamshinsa, Wadansu ma sukan yi amfani da ita a matsayin wani nau’in abinci da za su soya ta a cikin mai su hada ta da shinkafa ko acca ko wani hatsi da ya wadata a shiyyarsu. Wannan al’ada na da yawa a nahiyar Asiya, musamman ma yankin Larabawa da jinsin Indiyawa da Sinawa.
Kuma citta na kan gaba wajen yi da inganta ciye-ciye da shaye-shayen ban sha’awa a sassa da yawa a duniya. Bari mu fara daga gida Najeriya. Masu sayar da alawar gargajiya ta Hausa da ake cewa ‘alawar kara’ na yawo da busasshiyar citta suna ba mai saye domin ya hada da alawar ya tauna. Duk wanda ya taba yin wannan kwadon-bakan ya san irin gamsuwar da ya samu wajen wasashewar baki da makoshi. Haka kuma a wuraren da citta ta yawaita kamar Kaduna, lamurjen danyar citta ba bako ba ne; ana samunsa a wurin ‘yan talla a maciyar abinci da tituna da shaguna, har ma da manyan gidajen cin abinci. Sannan kuma masu yin kunun zaki da lamurjen lemon tsami da na zoborodo duk su kan sa citta a matsayin sinadari domin inganta lamurjensu.
Su kuwa a Turai da Amurka, su ne kan gaba wajen sarrafa citta domin yin irin wadannan kayayyakin ciye-ciye da shaye-shaye a masana’antunsu domin amfanin jama’arsu da kuma fitarwa zuwa sauran kasashen duniya. Su kan yi biskit iri-iri da citta, da burodin citta (ginger bread) da lamurjen citta (Ginger Ale da Ginger Lemon da dai sauransu) da alawoyi iri-iri na citta (kamar su Ginger candy) da shayin citta (Ginger tea) da sauran kayan shaye- shaye da yawa da suke yi da citta, irin su ‘Ginger drink’ da makamantansu
Citta a matsayin magani kuwa ruwan dare ce gama duniya. Kusan kowane jinsi a duniya na da wata kafa daya ko biyu, ko ma fiye ta sarrafa citta wajen yin magunguna daban bisa al’adarsa. Amma likitocin zamani sun hakikance cewa citta na maganin sanannun cututtuka goma ga dan Adam. Likitocin sun ce citta kalfiyan ce wajen warkar da mura, musamman ma idan an ci danyarta ko busasshiyarta da zuma, ko an yi shayinta an sha; an kuma ce tana maganin tashin zuciya inda aka tauna ta; za kuma ta iya tsayar da tari idan aka saka ta a baki ana tsotsa kamar alawa.
Likitoci kuma sun ce citta na maganin rudewar ciki, wanda ya hada da kumburin ciki da murdewa da kuma kuka da mutum ka iya ji a uwar hanjinsa; ana iya samun sakin wadannan al’amurra inda aka tauna citta. Sannan kuma citta na saukar da jini idan ya hau, idan mai wannan lalura ya sha citta a ruwa. Sun ce za kuma ta iya inganta gudanar jini a jika domin tana bude kafafen da jinin ke bi ta jijiyoyi. Sun kuma hakikanci cewa akwai wadansu sinadirai a cikin citta da ke kara kuzari ga maza.
Wannan dimbin amfani na citta ya sa take da farin jini a kasuwannin duniya. Idan Allah Ya kai mu makon gobe zan yi bayanin yadda dan kasuwa zai samu citta a kasar nan da yadda zai sarrafa ta domin kasuwanninmu na gida da kuma fitar da ita ya zuwa kasuwannin kasashen ketare.