Sarrafa Albarkatun Gona: Citta (2)

A makon jiya na fara bayanin yadda dan kasuwa zai sarrafa citta a matsayin daya daga cikin albarkatun gona da ake samu a kasar nan, domin sayarwa a kasuwannin cikin gida da na kasashen ketare. Na yi kuma bayanin dimbin amfanin citta a kasashen duniya wanda hakan ya sa take da kasuwa a kasashe da […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Citta (2)
Sarrafa Albarkatun Gona: Citta (2)

A makon jiya na fara bayanin yadda dan kasuwa zai sarrafa citta a matsayin daya daga cikin albarkatun gona da ake samu a kasar nan, domin sayarwa a kasuwannin cikin gida da na kasashen ketare. Na yi kuma bayanin dimbin amfanin citta a kasashen duniya wanda hakan ya sa take da kasuwa a kasashe da yawa a duniya. Ana kuma noma wadacciyar citta a Najeriya, inda ake samar da kimanin tan dubu 160 a shekara, wanda ya sa kasar ta kasance ta shida a sahun kasashe masu noma citta. Saboda yawan citta da ake nomawa ya wuce bukatar kasar, shi ya sa ta zama ta uku a duniya wajen fitar da ita zuwa kasuwannin ketare, inda take bin bayan kasashen China da Indiya.    
Na kuma samu karin bayani daga masu karatu a kan makalar makon jiyan, cewa ba wai jihohin Kaduna da Gombe da Bauchi da Binuwai da Nasarawa ba kadai ke noma citta ba, har ma da jihar Neja. To, dan kasuwa zai fara samun citta a wadannan wurare da ake noma ta tun daga watan Oktoba zuwa kakarta a watan Maris. Zai samu saiwar citta a matsayin danyarta, musamman ma a farkon zuwanta, zai kuma fara samun busasshiyarta da kakarta, har ma ya zuwa wani lokaci bayan nan.
    Akwai bukatar danya da busasshiyar citta a kasuwanninmu na gida da na waje, sai dai kowace bukata na tafiya da lokaci. Idan dan kasuwa na da niyyar cin kasuwar gida, to sai ya fara sayen cittarsa da zarar ta fara fitowa,domin sayarwa a kasuwannin gida. Kamar yadda sauran albarkatun gona ke fitowa da farashi mai tsada, kafin su fara sauka a sannu har ma farshinsu ya karye, to ita ma citta na da wannan tsarin. Saboda haka, abin da ‘yan kasuwa su ke yi shi ne, za su sayi citta su rika sayar da ita ga masu amfani da ita da farkon fitowarta. dan kasuwa zai kuma rika saya da danyar cittarsa yana kuma shanya wata tana bushewa domin sayarwa bayan kakarta, yayin da ta fara yin yawa farashinta yana saukowa.
    dan kasuwar da ya busar da cittarsa na iya sayar wa masu sararta domin sayarwa a kasuwannin gida, musamman ma na jihohin da ba a noma ta. Haka kuma zai iya sayar wa ‘yan kasuwa masu fitar da ita zuwa kasashen ketare. Shi ma dan kasuwan da ke da bukatar fitar da citta zuwa kasashen ketare zai fara sayen cittarsa a cikin tsakiyar kakarta, wato daga farkon watan Disamba, lokacin da farashinta ya fara sauka. dan kasuwa zai rika saye ya rika shanyawa y na tarawa. Mafi yawancin cittar da ake fitarwa kasashen waje busasshiya ce, a kan samu oda kadan daga kasashen waje na danyar citta.
    Wani abun dadi ga dan kasuwa mai fitar da citta zuwa kasashen ketare shi ne, akwai wadatacciyar rana da zai shanya ya busar da cittarsa a wannan shiyyar. Kuma lokaci ne da babu iska da za ta sa masa kura a cikin hajjarsa. Duk da haka dai zai yi kokarin yin shanyarsa a kebabben wuri mai tsabta da cittarsa ba za ta samu kura ba. Wadansu ‘yan kasuwa da ke fitar da citta zuwa kasashen ketare na amfani da na’urorin zamani wajen busar da cittarsu, amma kari da matsakaicin mai yin wannan harkar ba ya bukatar yin haka. dan kasuwa zai kuma iya sayen busasshiyar citta wurin wadanda suka ajiye ta domin fitarwa kasashen waje; Amma ya sani cewa wannan sai ta fi wadda ya busar tsada, saboda haka za ta rage masa riba.
    Ana zuba citta a cikin buhun roba ko na algarara mai nauyin kilo 50, wato buhu mai ‘L’. Sai dai mutanen da suka bada oda kan fadi a irin mazubi da nauyin cittar da suke bukata; misali mafi yawancin cittar da ake fita da ita zuwa Amurka a kwali ake fitar da ita, kuma mauyinta ba ya wuce tsakanin kilo 12 zuwa kilo 15. Farashin tan daya na citta a lokacin kakarta bay a wuci Naira dubu 150, tan din kuma yana kamawa daga dalar Amurka 1, 500 (N255,000) zuwa 1,700 (N340,000) ya danganta da mai saye da kuma kyan cittar. Cittar Najeriya na da kasuwa babba a kasashen Jamus da Ingila da Sifen da Amurka da Faransa da Nazaland da Rasha da Saudi Arabiya da dai sauransu.