Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi
A lokacin da nike share fagen wadannan jerin makalu na yadda dan kasuwa zai iya sarrafa albarkatun gona domin kaiwa kasuwanninmu na gida Najeriya da na kasashen ketare, na yi bayanin cewa albarkatun gona sun hada da dukkanin abubuwan amfani da za a iya samu daga kiwon dabbobi. Wadannan abubuwa sun hada da dabbobin kansu, […]
A lokacin da nike share fagen wadannan jerin makalu na yadda dan kasuwa zai iya sarrafa albarkatun gona domin kaiwa kasuwanninmu na gida Najeriya da na kasashen ketare, na yi bayanin cewa albarkatun gona sun hada da dukkanin abubuwan amfani da za a iya samu daga kiwon dabbobi. Wadannan abubuwa sun hada da dabbobin kansu, wato samar da su domin ci da sifiri da sauran ayyukan gida da na gona; da kuma sauran abubuwan da za a iya samu daga garesu, irin su nama da nono da fatunsu da kirgi da kahonninsu, har ma da taki da ake samu daga kashinsu.
A wannan makon zan yi bayani ne akan yadda dan kasuwa zai iya sarrafa fata da kirgin shanu a kasuwance domin sayarwa ya samu riba a kasuwanninmu na gida da na kasashen ketare. Na farko dai zan bambanta abin da ake nufi da fata da kuma abin da ake nufi da kirgi. Fata na nufin fatocin kananan dabbobi irinsu awaki da tumaki. Shi kuwa kirgi na nufin fatun shanu. A gargajiyance, ana amfani da fatu da kirgi wajen yin takalma da jikunkuna (irinsu alabe da zabira) da walki da buzu da salka da guga da ganguna da taiki da sirdin doki da linzamin doki da bulala (dorina) layu da kambu da kayayyakin ado na mata irin su cinko, da na adon kayan gida irin su faifai da kore da butoci da allunan karatu.
Kada in bar mai karatu da tambaya, domin na san mai karamin shekaru ba zai san wasu daga cikin kayayyakin da na lasafta a wannan jerin na baya ba, musamman ma idan bai tashi a karkara ba. Saboda haka ya zama dole in yi bayanin wasu daga cikinsu. Walki wata sutura ce da maza ke amfani da ita a gona ko wasu wurare na aikin karfi; fata ce da aka jeme, ta yi sumul ta na santsi. Sai kuma aka yi ta fadin da idan wanda aka yi ta dominsa ya daura ta a kugunsa za ta zagaya ta juyo, aka kuma yi mata siraran madaurai a geffanta biyu, domin daurawa. Sannan kuma tana da tsayin da za ta zo masa dab da gwiwarsa, wato walki tamkar gajeren wando ne a zamanance.
Ita kuwa salka, jika ce mai girma da zurfi da karamin baki, da aka yi ta domin zuba ruwan sha a matsayin guzuri, domin doguwar tafiya. Fatake masu safara tsakanin garuruwa na daukar salka domin guzurin ruwa don kada ruwan ya yanke musu a daji inda babu. Duk da zuwan mota da wadatarta ya kashe fataucin tafiyar kasa inda ake dora wa dabbobi kaya a bisu zuwa garuruwa, har yanzu ana samun salka a rataye a jikin manyan motoci masu keta Hamada a cikin kasar Nijar, wadanda ke guzurin ruwa a cikin salkunan domin karancinsa a cikin Hamada.
Taiki kuwa, wani mazubi ne da ke da girman gaske da ake zuba tsabar amfanin gona, musamman ma gyada a dorawa takarkari (yaron sa, ko bajimi) ko kuma jaki, domin kaiwa kasuwa. Taiki na da siffar mangala da ake dorawa jaki, wacce ake yi da kaba, sai dai shi taiki da kirgi ake yunsa kuma ya fi mangala girma sosai kuma bakinsa a tsuke yake sabanin na mangala da ya ke a bude. Cinko kuwa wani abu ne mai tsayi da mata ke sakawa a wuya ya kawo kirjinsu, wanda ake yi da fata da tsabar kudi (kwabbai da sulalla da tarare) irin na zamanin da. Wadannan tsabar kudi na kasancewa wadanda aka yi da karafa masu kyau irin su tagulla da goran ruwa da azurfa da makamantansu. An dade da daina amfani da cinko, amma har yanzu ana samun sa a wurin matan Fulani.
Zan tsaya anan. Idan Allah Ya kai mu makon gobe zan duba ma’aikatar yin wadannan kayayyaki a gargayance, wato majema da kuma irin bukatar da ake da su a kasuwannin gida da na waje, wato kasuwarsu. Zan kuma duba masana’antun zamani da ke sarrafa fata da kirgi a zamanance da irin kayayyakin da suke samarwa a kasuwannin gida da na kasashen waje. Sannan in duba kasuwar kirgi da fatu, da kuma ta masana’antu da ke sarrafa su.