Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (10)
A wannan makon zan yi bayani ne a kan dabara ta biyar daga cikin dabarun harkar fata da kirgi shida a matakin farko na harkar, wato Safarar Fata da kirgi. Sauran dabaru hudu da na yi bayani a kan su a makalu makonnin baya su ne, Kyan fata da kirgi da Farashin fata da kirgi […]

A wannan makon zan yi bayani ne a kan dabara ta biyar daga cikin dabarun harkar fata da kirgi shida a matakin farko na harkar, wato Safarar Fata da kirgi. Sauran dabaru hudu da na yi bayani a kan su a makalu makonnin baya su ne, Kyan fata da kirgi da Farashin fata da kirgi da Jarin dan kasuwa mai irin wannan harka, da kuma Adanawa da sarrafa fata da kirgi. Sauran dabarar da ta rage daga cikin shidar da na lissafa a farkon jerin wannan makala ta Sarrafa Fata da kirgi a matsayin albarkatun gona, ita ce Babban dillalin da dan kasuwa zai sayar wa fata da kirgin da ya saya.
Safara a nan na nufin daukar wani ko sayen wani abu daga wurin da ake samun sa zuwa wuri ko wuraren da ba a samunsa. Shi kansa kasuwanci ya dogara ne gaba daya a kan sani ko basira ta sanin inda za a samu wani abu domin wadata shi a wurin da ake da karancinsa. Yana kuma iya kasancewa basirar sanar da mai saye inda wata haja take domin ya saya; ko kuma sani ko basirar hada mai saye da mai sayarwa ba tare da motsa hajar da za a saya ko za a sayar ba, ko kuma yanayin duk guda biyu. Misali wanda zai sayar da gida ko fili ko kuma zai bayar da su haya, zai nemi dillalin gida da filaye domin ya san masu neman saye ko hayar gidaje da filaye. Shi kuma mai sayen gida ko fili, ko kuma mai neman hayar daya daga ciki zai nemi dillalin gidaje da filaye domin haka, inda wannan dillalin zai hada mai sayarwa ko mai bayar da haya da mai saye ko mai karbar haya. Haka ma matafi da dan kamasho da mai mota, ko kuma mai tafiya kasashen waje da ejen (Trabel Agent da Turanci) da kamfanonin jiragen sama.
To mu dawo safarar fata da kirgi. Kamar yadda na yi shimfida a kasidar farko ta wannan makala, dan kasuwa mai niyyar shiga wannan harka a matakin farko, wato matakin mai karamin jari da zai sayi fata da kirgi ya sayar wa dillali mai matsakaicin jari, sai ya yi nazarin inda zai sayi wannan hajar da inda zai sayar da ita. To a nan ne safara ta taso, inda abu mafi mahimmanci a cikinta shi ne, yadda za a tafiyar da wannan haja daga wurin da aka saye ta ya zuwa inda za a sayar da ita, ko kuma inda za a tara ta, daga baya kuma a kai ta ga mai saye. Muhimmancin nazarin wannan mataki shi ne, wani babban bangare na jarin dan kasuwa na shiga wannan mataki wajen sufurin hajar da ya saya kafin ya kai ga wurin da zai sayar da ita.
Abin yi a nan yayin da dan kasuwa zai shiga wannan harka sai ya nazarci yanayin wurin da ya ke da zama, wato wurin da zai yi wannan harkar, sannan ya nazarci nisan wurin da zai sayi hajar da kuma wurin da zai sayar da ita. Idan mai karatu na biye da ni, zai iya tunawa a kasidar makon shekaranjiya na nazarci matsayin dan kasuwa guda uku a cikin wannan harkar, domin girma da kuma yadda zai sarrafa jarinsa ya samu ingantacciyar riba kamar haka:
dan kasuwar da zai sayi fata da kirgi a garin da yake da zama ya kai wa dillalin da zai saya a cikin garin daya, wato inda dan kasuwar yake; dan kasuwar da zai sayi fata da kirgi a garin da yake da zama ya kai wa dillali a wani gari, sai kuma dan kasuwar da zai sayi fata da kirgi a wani garin da ba inda yake da zama ba, ya kuma sayar da ita a wani garin.
Zan tashi da bayanin wadannan yanayin idan Allah Ya kaimu makon gobe.