Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (11)
Zan ci gaba da dabara ta biyar daga cikin dabarun harkar fata da kirgi guda shida a matakin farko na harkar, wato Safarar Fata da kirgi. Wadannan dabaru guda shida sun hada da dabaru hudu da na yi bayani a kan su a makalun makonnin baya, wato Kyan fata da kirgi da Farashin fata da […]

Zan ci gaba da dabara ta biyar daga cikin dabarun harkar fata da kirgi guda shida a matakin farko na harkar, wato Safarar Fata da kirgi. Wadannan dabaru guda shida sun hada da dabaru hudu da na yi bayani a kan su a makalun makonnin baya, wato Kyan fata da kirgi da Farashin fata da kirgi da Jarin dan kasuwa mai irin wannan harka, da kuma Adanawa da sarrafa fata da kirgi. Ita kuwa dabara ta shida da zan yi gaba ita ce Babban dillalin da dan kasuwa zai sayar wa fata da kirgin da ya saya. Idan kuma mai karatu na biye da ni zai iya tunawa na tsaya a makon jiya a kan ma’anar safara da mahimmancinta a wannan harka da kuma yadda dan kasuwa zai duba matsayin wurin da yake da zama da kuma kasuwar da zai sayi fata da kirgi, da kuma inda babban dillalin da zai sayar masa da hajjarsa yake da zama.
Idan mai karatu bai manta ba, a yayin da nake tattauna karfin jarin dan kasuwa a matsayin dabara ta uku daga cikin shida ta harkar fata da kirgi, na yi bayanin yadda dan kasuwa zai yi amfani da wannan matsayi na wurin zamansa domin kyakkyawan amfani da jarinsa bisa la’akari da nisan kasuwarsa ta fata da kirgi da kuma wurin zaman babban dillalinsa, domin samun ingantacciyar riba. To wannan al’amari ba zai sauya a bangaren safarar fata da kirgi ba, domin kudin sufuri wanda shi ne kashin bayan wannan dabara, na da tasiri kwarai wajen sarrafa jarin dan kasuwar da ke cikin wannan harka.
Zan waiwaya baya a cikin makalar makon jiya domin in yi wa mai karatu tilawa a kan matsayin wurin zaman dan kasuwa da ke wannan harkar, kafin in dora masa sabon darasi a kan wannan dabara. A makalar makon jiyan na ce, abin lura a dabarar safarar fata da kirgi yayin da dan kasuwa zai shiga wannan harka shi ne, yin nazarin yanayin wurin da yake da zama, wato wurin da zai yi wannan harkar, sannan ya nazarci nisan wurin da zai sayi hajar da kuma wurin da zai sayar da ita. Idan mai karatu na biye da ni, zai iya tunawa a kasidar makon shekaranjiya na nazarci matsayin dan kasuwa guda uku a cikin wannan harkar domin girma da kuma yadda zai sarrafa jarinsa ya samu ingantacciyar riba kamar haka: dan kasuwar da zai sayi fata da kirgi a garin da yake da zama ya kai wa dillalin da zai saya a cikin gari daya, wato inda dan kasuwar yake; dan kasuwar da zai sayi fata da kirgi a garin da yake da zama ya kai wa dillali a wani gari, sai kuma dan kasuwan da zai sayi fata da kirgi a wani garin da ba inda yake da zama ba, ya kuma sayar da ita a wani garin.
Saboda haka, dan kasuwar da ya samu kansa a matsayi na farko ba shi da matsalar sufuri kamar sauran ’yan kasuwar da suke mataki na biyu da na uku; dan kasuwar da ke matsayin farko idan ba a manta ba, shi ne wanda zai sayi fata da kirgi a garin da yake da zama ya kuma kai wa dillalin da zai saya a cikin gari daya, wato inda dan kasuwar yake. To kamar yadda na yi bayani a makalar Jarin dan kasuwa, a wannan karon ma shi wannan dan kasuwa zai sayi babur ko Keke Napep da aka fi sani da A Daidaita Sahu, a wasu wuraren, domin daukar hajar da ya saya idan yana da ikon yin hakan. Idan kuwa ba shi da karfin jarin yin hakan, dan kasuwa zai rika tara hajarsa a cikin yinin da ya saya, sannan idan yamma ta yi, ko lokacin da ya ga ya gama saye, sai ya dauke ta a motar haya ko babur din haya ya kai wa babban dillali mai saye.
dan kasuwar da ke wannan matsayi na samun ragowar kudin sufuri fiye da sauran da ke matsayi na biyu da na uku. Sai dai yana da wani babban kalubale, an fi samun kananan ’yan kasuwa masu harkar fata da kirgi a wannan matsayin, saboda kusanci da babban dillali. Wani lokaci ma wadanda suka yanka dabbar na iya kai wa babban dillali fatarsu ko kirginsu, su tsallake karamin mai saye domin samun babban farashi. Haka kuma da Sallah Babba da ake yanka raguna da shanu akan samu masu sayen fata da kirgi na shekara- shekara suna shiga harkar a daidai wannan lokacin. Irin wadannan yanayin na rage yawan fata da kirgi da dan kasuwar da ke wannan matsayi zai samu, ko kuma su tayar da farashin hajar inda ribarsa za ta ragu.
Dabara ga dan kasuwa a wannan matsayi ita ce, ya rike abokan cinikinsa ya rika kyautata musu, musamman ma wajen farashin da yake sayen fata da kirgi daga wurinsu, yadda wani mai saye ba zai ture shi daga gare su ba; ko kuma masu sayar masa su wuce shi su kai wa babban dillali. Zan ci gaba idan Allah Ya kai mu makon gobe.