Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (12)
A wannan makon zan ci gaba da bayani a kan dabara ta biyar daga cikin shida ta sayen fata da kirgi a matakin farko, wato dabarar sufuri, wacce na fara tattaunawa a makon jiya karkashin safara. Dabaru hudu da na yi bayani a kansu a makalun makonnin baya sun hada da Kyan fata da kirgi […]
A wannan makon zan ci gaba da bayani a kan dabara ta biyar daga cikin shida ta sayen fata da kirgi a matakin farko, wato dabarar sufuri, wacce na fara tattaunawa a makon jiya karkashin safara. Dabaru hudu da na yi bayani a kansu a makalun makonnin baya sun hada da Kyan fata da kirgi da Farashin fata da kirgi da Jarin dan kasuwa mai irin wannan harka, da kuma Adanawa da sarrafa fata da kirgi. Ita kuwa dabara ta shida da zan yi a gaba ita ce Babban dillalin da dan kasuwa zai sayar wa fata da kirgin da ya saya.
A wannan dabara ta biyar da na fara batunta a makon jiya, na duba yanayin dan kasuwa da zai kasance yana zaune a gari daya da kasuwar da yake sayen hajarsa da kuma babban dillalin fata da kirgi da zai sayar wa wannan hajar. Kuma idan mai karatu bai shafa’a ba, zai iya tuna cewa na bayyana lagwadar hakan da kuma irin kalubalen da irin wannan dan kasuwa zai iya fuskanta. Na kuma ba shi shawarar yadda zai iya shawo kan irin wannan kalubale.
Shi kuwa dan kasuwar da ke cikin yanayi na biyu a matakin farko na harkar fata da kirgi, shi ne, wanda zai kasance yana zaune a garin da yake sayen fata da kirgi, amma babban dillalin da zai sayar wa yana wani garin daban. A nan, ya zama dole dan kasuwa ya sayi hajarsa ya tara kafin ya nemi mota ya zuba ya kai wa babban dillalin da zai saya. To idan muka lura da wannan lamari, ya zama dole dan kasuwa ya nemi wurin adana hajarsa, sannan kuma ya bukaci motar da za ta dauka masa wannan hajar zuwa garin da zai sayar da ita. Kuma idan kasuwarsa ba babba ba ce, wacce a karo daya zai iya samun isassun fata da kirgi ya saya a rana daya, to ya zama dole ya fara sarrafa hajarsa don kada ta lalace kafin ya kai ta wurin masu saya. Na yi wannan bayani yayin da na ke tattauna dabarar adana fata da kirgi.
Ya zama dole dan kasuwa da ke wannan yanayi ya kasance jarinsa na da kauri fiye da na dan kasuwa da ke a yanayin farko. Sannan kuma ya zama dole ya daidaita farashinsa na sayen fata da kirgi domin ya fitar da wahalhalun da zai yi wa hajarsa kafin ya kai ta wurin masu saya. Saboda hidindumin da na bayyana da irin yadda dan kasuwa zai yi wa hajarsa zai kasance ya rike kudi mai dan yawa bayan ya sayi hajarsa, domin wadannan hidindumu, sabanin dan kasuwar a matsayin farko, wanda zai sayi hajarsa daga kasuwa ya wuce kai tsaye zuwa wurin babban dillalin da zai sayarwa. Kamar yadda na fada a baya, farashin da zai sayi hajarsa ba zai kasance daya da na wanda zai yi mata hidima ba; idan mai karatu zai tuna, na yi bayanin a makalar farko cewa ribar fata da kirgi na samuwa ne daga farashin da dan kasuwa ya sayi hajarsa, tun da farashin da zai sayar tsayayye ne, sabanin tsarin sauran harkoki inda farashin sayarwa ke haifar da riba. Kuma idan irin wannan dan kasuwa na da sukunin sayen motar kansa da zai yi wannan harkar zai fi a gare shi, domin zai samu saukin tafiyar da ita, kuma zai samu ragin kudin da zai rika biyan motar haya. Wannan zai inganta ribarsa kwarai da gaske.
Rashin sarari ba zai bar ni in fara tattauna matsayi na uku na dan kasuwar da zai yi wannan harka a matakin farko ba, wato dan kasuwar da kasuwar da zai sayi hajarsa da mazaunin da babban dillalin da zai sayar wa suke garuruwa daban-daban da inda yake zaune yake gudanar da harkarsa.