Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (13)

Zan tattauna matsayi na uku, kuma na karshe a cikin dabara ta biyar daga cikin shida ta harkar fata da kirgi, wato dabarar Safara. A wannan matsayi dan kasuwar da zai yi wannan harka a matakin farko, na zaune ne a inda kasuwar da zai sayi hajarsa da mazaunin da babban dillalin da zai sayarwa […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (13)

Zan tattauna matsayi na uku, kuma na karshe a cikin dabara ta biyar daga cikin shida ta harkar fata da kirgi, wato dabarar Safara. A wannan matsayi dan kasuwar da zai yi wannan harka a matakin farko, na zaune ne a inda kasuwar da zai sayi hajarsa da mazaunin da babban dillalin da zai sayarwa ke, da inda yake zaune yake gudanar da harkarsa. 

Na kammala bayani a kan dan kasuwa da ke matsayi na biyu na wannan dabarar, a makon jiya, inda dan kasuwa ke zaune yake tafiyar da harkarsa a gari daya da kasuwar da yake sayen hajarsa, amma gari daban da inda zai sayar wa babban dillalinsa.
Idan kuma mai karatu na biye da ni zai iya tuna wadannan dabaru hudu daga cikin shida na harkar fata da kirgi a matakin farko da na tattauna a makonnin baya, kamar haka: Kyan fata da kirgi da Farashin fata da kirgi da Jarin dan kasuwa mai irin wannan harka, da kuma Adanawa da Sarrafa fata da kirgi. A wannan makon zan duba dabara ta shida, wato Babban dillalin da dan kasuwa zai sayar wa fata da kirgin da ya saya.
Irin wannan dan kasuwa zai fuskanci hidindumun da zai yi wa hajar da zai saya kafin ya kai ta kasuwa, fiye da sauran ’yan kasuwar da ke matsayi na farko da na biyu. Na farko dai dan kasuwa zai kai kansa kasuwar da zai sayi wannan hajar, sannan kuma a mafi yawan lokuta zai dauki wannan hajar zuwa garin da yake da zama, ya kuma ke tafiyar da harkarsa kafin ya kai ta garin da babban dillalinsa yake domin sayarwa. A kadan daga cikin lokuta ne akan samu irin wannan dan kasuwa ya yi dacen iya daukar hajarsa kai-tsaye daga kasuwar da ya sayi hajarsa ya zuwa garin da babban dillalinsa yake ya sayar masa.
Kamar dan kasuwar da yake matsayi na biyu a matakin farko na wannan harka, shi ma dan kasuwa da ke matsayi na uku na wannan mataki zai fuskanci hidindumun sufuri da sarrafa hajarsa fiye da dukkan ’yan kasuwan da ke wannan matakin. Idan aka tuna, dan kasuwa na matsayi na biyu na fuskantar kudin sufurin kayansa daga garin da kasuwar da ya sayi kayansa zuwa garin da yake da zama, kuma garin da babban dillalinsa yake da zai sayar wa hajarsa. Wata hidima kuma ga dan kasuwar da yake a matsayi na uku ita ce sake daukar wasu zuwa garin da babban dillali yake, daga garin da yake da zama. Kuma kamar dan kasuwa na matsayi na biyu, zai iya fuskantar yanayin da lallai sai ya adana ya kuma sarrafa wannan hajar kafin ya dauke ta zuwa wurin sayarwa.
To dukkanin wadannan hidundumu na bukatar kudi, saboda haka dole jarin wannan dan kasuwa ya fi na sauran ’yan kasuwar da ke sauran matsayin suke tafiyar da wannan harkar. Sannan kuma farashinsa dole sai ya bambanta da nasu wajen saye, domin kamar yadda na sha fada a wannan filin, farashin sayar da fata da kirgi tsayayye ne, riba na fita ne daga kokarin da dan kasuwa zai yi wajen samun rangwame daga masu sayar masa kayan. To tun da Farashin wannan dan kasuwa zai kasance kasa da na sauran, yana iya samun matsaloli wajen sayen kaya, inda zai ci kasuwa da ’yan kasuwar da ke matsayi na daya da na biyu, wadanda za su iya fin sa samun kaya tun da farashinsu ya fi kauri.
Sai dai kuma da wuya a samu dan kasuwa na matsayin farko a wannan kasuwa, wato inda mai sayen wannan hajar ke gari daya da kasuwar hajar da kuma garin da babban dillali ke zaune. Babu basira ga dan kasuwa na matsayi na uku ya yi harka a wannan kasuwar, sai dai in zai mayar da al’amarinsa matsayin farko inda zai shigo garin ya sayi hajar ya sayar wa babban dillali kai-tsaye.
Zan tashi daga nan in Allah Ya kaimu makon gobe.