Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (15)

A wannan makon zan yi bayani a kan yadda dan kasuwa zai shiga harkar fata da kirgi a matsayin Babban Dillali. Idan ba a manta ba na raba harkar fata da kirgi gida uku yayin da nake shimfidar bayani a farkon wannan makala ta harkar fata da kirgi, kamar haka: Na farko, karamin dan kasuwa […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (15)
Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (15)

A wannan makon zan yi bayani a kan yadda dan kasuwa zai shiga harkar fata da kirgi a matsayin Babban Dillali. Idan ba a manta ba na raba harkar fata da kirgi gida uku yayin da nake shimfidar bayani a farkon wannan makala ta harkar fata da kirgi, kamar haka: Na farko, karamin dan kasuwa da zai sayi fata da kirgi kai-tsaye daga hannun wadanda suka samar da su; na biyu, Babban Dillali da kananan ’yan kasuwa za su sayar wa fata da kirgi, na hudu, wato kamfanonin da manyan dillalai za su sayar wa fata da kirgi domin su jeme su yi amfani da ita wajen yin kayayyaki, domin amfani da su a gida Najeriya, ko kuma sayar da su a kasashen ketare. Irin wadannan kamfanoni na jima za su kuma iya sayar da fata da kirgin da suka sarrafa ga kamfanoni a Najeriya da na kasashen waje wannan haja tasu domin mayar da ita abubuwan amfani a gida da masana’antu.
To idan mai karatu na biye da ni zai ga cewa wannan fili na da al’adar dauka da bayanin kowace harka a karami da matsakaicin mataki, domin amfanin kanana da matsakaitan ’yan kasuwa. Saboda haka na fara da tattauna yadda za a iya tafiyar da wannan harka a karamin mataki, inda na share makonni ina yin bayanai, ina kuma bayar da shawarwari a kan yadda za a iya tafiyar da ita a cikin nasara. Shi ya sa zan duba yadda dan kasuwa zai iya shiga wannan harka a matsakaicin mataki, wato a matsayin matakaicin dan kasuwa mai harkar fata da kirgi inda zai zamanto Babban Dillalin fata da kirgi.
dan kasuwa na bukatar samun babban jarin da zai shiga wannan harkar a matsayin babban dillali. Wannan jari ma zai iya kasancewa daga Naira miliyan 10 zuwa Naira miliyan 100, ya danganta da karfin dan kasuwa da kuma fadin kasuwarsa. Fadin kasuwa na nufin yawan kananan ’yan kasuwa da yake tsammanin za su iya kawo masa kaya ya saya, da kuma wadatar fata da kirgi a shiyyar da zai yi wannan kasuwancin. Zan yi wa dan kasuwa matashiyar wani tsokaci da nake yi a kullu-yaumin in zan fara bayanin wata sabuwar harka, musamman ma idan tana bukatar babban jari, wato nazarin yanayin kasuwa kafin a fara harka. A nan, kafin dan kasuwa ya zuba jari irin wannan cikin harkar fata da kirgi, ko ma wacce harka ce, sai ya nazarci kasuwar wannan harkar.        
Nazarin kasuwar fata da kirgi domin zuba jari a matsayin babban dillali ya hada da la’akari da samuwar wannan hajar da kimanin ta a shiyyar da dan kasuwa zai yi harkar; mutum nawa ne ke yin wannan harka a kuma wannan matsayi a shiyyar da dan kasuwa zai shige ta? Kimanin kananan ’yan kasuwa nawa ke wannan sana’ar a shiyyar, kuma mene karfin jarinsu da kwarewarsu a harkar?  Wane irin wuri da kuma wadanne irin kayan aiki da ma’aikata yake bukata domin yin wannan harka? Wane kamfanin jima zai sayar wa fata da kirginsa idan ya saya? Da dai sauran wasu abubuwan lura domin samun nasarar harkar.
 Zan duba in kuma bayar da shawarwari a kan wadannan al’amura da ya kamata dan kasuwa ya lura da su kafin ya shiga harkar fata da kirgi a matsakaiciyar harka ta babban dillali, inda zan fara da samuwar wannan hajar a shiyyar da dan kasuwai zai yi wannan harka. Kafin in yi haka, zan yi wa mai karatu bayanin sharar fagen matsayin babban dillali a cikin wannan harka ta sayen fata da kirgi.
Shidai babban dillali zai kasance yana hulda da wani ko wasu manyan kamfanonin jimar fata da kirgi da za su sayi hajarsa. A mafi yawancin lokuta, dillali na kasancewa yana hulda ne da kamfanin jima guda daya. Wannan kamfani zai ba shi da sauran abokan huldar kamfani wani farashi tsayayye da za su sayi fata da kirgi daga abokan huldarsu. Kamfanonin za su sanar da manyan dillalansu idan an samu bambancin farashi, wasu lokutan ma sukan tsayar da farashi daga zaman shawara da suka yi da manyan dillalansu. Shi kuma babban dillali zai sanar wa kananan ’yan kasuwa wannan farashi da yake sayan kaya a hannunsu.