Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (16)
Zan kammala wannan makala ta harkar fata da kirgi a wannan makon, inda zan duba in kuma bayar da shawarwari a kan irin al’amuran da suka kamata dan kasuwa ya lura da su kafin ya shiga harkar fata da kirgi a matsakaiciyar harka ta babban dillalin fata da kirgi. Na fara da bayani a kan […]

Zan kammala wannan makala ta harkar fata da kirgi a wannan makon, inda zan duba in kuma bayar da shawarwari a kan irin al’amuran da suka kamata dan kasuwa ya lura da su kafin ya shiga harkar fata da kirgi a matsakaiciyar harka ta babban dillalin fata da kirgi.
Na fara da bayani a kan samuwar wannan hajar a shiyyar da dan kasuwai zai yi wannan harka, a makon da ya gabata. Na kuma yi wa mai karatu bayanin sharar fagen matsayin babban dillali a cikin wannan harka ta sayen fata da kirgi, inda na ce babban dillali zai kasance yana da hulda da wani ko wasu manyan kamfanonin jimar fata da kirgi da za su sayi hajarsa, inda mafi yawancin lokuta, dillali na kasancewa yana hulda ne da kamfanin jima guda daya ne.
Wannan kamfani zai ba shi da sauran abokan huldar kamfani wani farashi tsayayye da za su sayi fata da kirgi daga abokan huldarsu, Kamfanin zai sanar da manyan dillalansu idan an samu bambanci farashi, wasu lokutan ma sukan tsayar da farashi daga zaman shawarar da suka yi da manyan dillalansu. Shi kuma babban dillali zai sanarwa da wannan farashi ga sauran kananan ’yan kasuwa da ya ke sayan kaya daga hannunsu.
Na kuma yi bayanin kasancewar dan kasuwa ya tanadi babban jari domin shiga wannan harka a matsayin babban dillali, inda na ce wannan jari zai kama daga Naira miliyan goma zuwa Naira miliyan dari. Irin wannan babban jari ya zama dole domin dan kasuwa ya kasance yana shirye a kowanne lokaci ya sayi kaya ya biya ba tare da jeka-ka- dawo ba. Sannan dole dan kasuwar da zai tafiyar da wannan harka a matsayin babban dillali ya tanadi motocin da za su yi masa jigilar kayansa tsakanin wuri ko garin da yake tafiyar da wannan harka zuwa kamfanin da zai kaiwa kayan. Daga cikin wannan jarin zai tanadi sauran kayan aiki irin su babban sikelin awo da wurin sayen wannan kaya da wurin sarrafawa da shanya, da kuma biyan ma’aikatan da za su yi wannan hidima.
Wannan jari na dan kasuwa ya danganta da yawan hajar da zai iya samu daga shiyyar da zai yi wannan harka, kamar yadda na yi bayani a makon jiya. Yawan fata da kirgi da babban dillali zai iya samu a shiyyar kasuwancinsa zai yi daidai da girman jarin da zai tanada. Haka kuma karfin jarin kananan ’yan kasuwar da zai yi hulda da su a shiyyar zai kasance manuniya ga irin yawan jarin da zai nema domin wannan harka. Misali, babban dan kasuwa zai kasance mai bai wa wasu daga cikin kananan ’yan kasuwan da yake hulda da su kudi (wato adibans) su samo masa wannan hajar, musamman ma lokacin babbar Sallah, lokacin da fata da kirgi ke saniya da yawa har ta fice karfin jarin kananan ’yan kasuwa masu harkar fata da kirgi a shiyyar, wanda zai kasance sai sun nemo dauki daga manyan dillalan da suke sayar wa hajarsu.
Sannan dan kasuwa na iya kasancewa ba shi kadai ne babban dillalin fata da kirgi a shiyyar da yake wannan harka ba. Yayin da dan kasuwa ya samu kansa a wannan hali to ya zama dole ya kasance da isasshen jari domin tunkarar wannan kalubale. Na farko dai kamar yadda na saba bayani a yanayi irin wannan, dole sai ya kasance yana kyautata wa abokan huldarsa masu kawo masa kaya ya saya, domin janye hankalinsu daga hulda da takwarorin harkarsa. Kyautatawa a nan ta hada da ba su farashi na kwarai da biyan su a kan lokaci da auna kayansu bisa gaskiya a biya su yadda ya kamata da ma dubawa da karbar kayan bisa ka’ida ba tare wulakanci wajen fitar da zaren fata da kirgi ba.
Shi ma babban dillali zai yi amfani da basirarsa wajen zaben kamfanin jima da zai hulda da shi wajen sayar da kayansa. Babban abin la’akari da shi a nan shi ne karfin jarin kamfanin da kuma mutuncin masu shi da na masu gudanar da shi.