Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (2)
Wasu masu karatun wannan filin sun jawo hankalina akan wata hanya guda daya mai mahimmancin gaske da ban yi maganarta kuma na lissafata ba, a cikin hanyoyin da ake amfani da fata da kirgi a gargajiyence, ita ce ganda. Kafin a tunatar da ni wannan ma kuwa, a makon da ya gabata na yi muku […]
Wasu masu karatun wannan filin sun jawo hankalina akan wata hanya guda daya mai mahimmancin gaske da ban yi maganarta kuma na lissafata ba, a cikin hanyoyin da ake amfani da fata da kirgi a gargajiyence, ita ce ganda. Kafin a tunatar da ni wannan ma kuwa, a makon da ya gabata na yi muku alkawarin cewa a wannan makon zan duba ma’aikatar yin wadannan kayayyakin fata da na kirgi da na lasafta amfaninsu a gargajiyance, wato majema da kuma irin bukatar da ake dasu a kasuwannin gida da na waje, wato karfin kaswarsu. Na kuma yi alkawari zan duba masana’antun zamani da ke sarrafa fata da kirgi a zamanance da irin kayayyakin da su ke samarwa a kasuwannin gida da na kasashen waje.
To, faduwa ta zo daidai da zama, domin ita kanta ganda wata cimaka ce ta gargajiya, kuma tunamin in yi batun ta ya zo daidai lokacin da zan yi bayani akan masana’antar sarrafa fata da kirgi. Ana samar da ganda daga kirgi a matsayin nama domin farfesu ko sinadarin miya. Ba a yin ganda da fata. Kuma idan mai karatu na tafiye biye da ni, zai iya tunawa cewa na bambanta fata da kirgi a makalar da na yi a makon da ya gabata, inda na ce kirgi na nufin fatar manya dabbobi, musamman ma shanu, ita kuwa fata na nufin fatun kananan dabbobi kamar awaki da tumaki.
Mai karatu zai ga na kasa amfanin ganda gida biyu, kashin da ya yi daidai da na jinsi biyu da ke amfani da shi, wato Hausawa da sauran kabilun Arewa a gefe daya, da kuma Yarabawa da sauran kabilun kudancin kasarnan a daya gefen. Haka kuma yin ganda ya danganta da bukatar wannan kashi biyu na jinsunan ’yan Najeriya. Misali, gandar da ake amfani da ita a Arewa ana babbaka fatar saniya ne da zarar an fede ta. Sai a yanyanka ta irin girman da ake bukata domin sayarwa masu bukata. Kamar yadda na yi bayani a baya, irin wannan ganda ana yin farfesu da ita, musamman ma domin mata masu jego, ko mutanen da ke fama da mura, ko kuma a sha a nishadance.
Launin ganda ta biyu da ake amfani da ita a matsayin sinadarin miya, ana kuma kiran ta ‘Kpomo’ko ‘Pomo’. Yadda ake yin wannan ganda ya bambanta da yadda ake yin waccan da na fara bayanin ta a baya. Ana shanya kirgin da za a yi pomo da shi ya bushe kayau, bayan an babbake shi. Bushewar wannan kirgi na daukar lokacin da ka iya kaiwa kimanin sati ko fiye, ya danganta da yanayin shekara da samun hasken ranar da aka iya samu. Kamar yadda ake yin waccan gandar ta farko, ita ma wannan za a yayyanka kirgin daidai bukata a barbade shi da gishiri, domin gudun kada ya rube, sai a shanya. Za a wanke shi kwarai da gaske saboda dadewar da yayi ana shanya shi, saboda kura da ka iya samunsa yayin da ake ta famar shanya shi. Dogon lokacin da ake dauka wajen shanyar da ake yi wa wannan ganda ya zama dole domin mafi yawancin wannan ganda a Arewacin Najeriya ake samar da ita a kuma kaita kudancin kasar ga masu amfani da ita.
Ba kuma a nan sarrafa wannan ganda ta tsaya ba, wadanda suka saye ta a wannan matsayi ba masu amfani da ita ba ne, dillalai ne da za su ci gaba da sarrafata, domin sayarwa ga wadanda za su saya su yi amfani da ita. Da farko dai ana yanka kirgin wannan ganda kimanin fadin hannu a shanya ta, ta bushe a saka ta cikin buhuna a dinke a kai kasuwa walau a Arewa ko a kudancin kasarnan. Zan tashi daga nan idan Allah Ya kaimu makon gobe.