Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (3)
Mukalar da ta gabata da na yi ta a kan ganda (kpomo ko pomo) da ta fado daidai lokacin da ake mahawara a kan rade-radin yunkurin Gwamnatin Tarayya na haramta cin ganda a kasar nan. Wannan magana ta samo tushe daga kiran da Ministan Albarkatun Gona da Raya Karkara, Dokta Akinwumi Adesina yi wa gwamnati […]

Mukalar da ta gabata da na yi ta a kan ganda (kpomo ko pomo) da ta fado daidai lokacin da ake mahawara a kan rade-radin yunkurin Gwamnatin Tarayya na haramta cin ganda a kasar nan. Wannan magana ta samo tushe daga kiran da Ministan Albarkatun Gona da Raya Karkara, Dokta Akinwumi Adesina yi wa gwamnati da samar da dokoki masu ingancin gaske da za su haramta wa jama’ar Najeriya cin ganda, domin wadata masana’antun kasar da fata da kirgin da za su sarrafa wajen yin kayayyakin da za su sayar a kasuwannin gida da na waje. Ministan ya yi wannan kiran ne a bikin hadin-gwiwa karo na uku na Masana Kimiyyar Dabbobi (Animal Science Association) da Tsangayar Kimiyyar Dabbobi (Institute of Animal Science) da aka yi a garin Ibadan.
Wannan kira na minista ba cece-kuce kadai ya kawo a kasar nan ba, ya ma fito da irin dumbin jama’ar da ke cin ganda daga sassa daban-daban na kasar nan da kuma mahimmancin ganda ga jama’a daban-daban. Haka kuma al’amarin ya fito da hanyoyi daban-daban na ta’ammali da ganda a launikan abincin kabilun kasar nan. Masu adawa da wannan kira na minista, wadanda suka hada da maciya gandar da masu yin ta da sayar da ita, na cewa ministan ba shi da cikakkiyar masaniya game da wannan hujja da ya yi magana a kan ta; suna cewa cin ganda ba ya rage yawan kirgin da ke tafiya masana’antu, domin a mafi yawancin lokuta ana yin ganda ne da damejin kirgi ko kirgi marar inganci, wato launin kirgi kashi biyu ne wadanda masana’antu ba sa bukata wajen tafiyar da sana’arsu. Wannan la’akari da masoya ganda suke yi, ya yi wa wannan fili matashiya wajen yi wa dan kasuwa bayani da ba shi shawarwari wajen sayen fata da kirgi daga tushensu.
Wata hujja da maciya ganda kuma ke gabatarwa ita ce, likitoci na ba mutane masu tarun shekaru da mutane masu lalurar maiko a jika, ko masu kiba shawarar cin ganda maimakon jan nama domin lafiyarsu. Sai dai ma’abota cin ganda, musamman ma ’yan asalin kudancin kasar nan, na kaurace wa wani fanni na kiran da ministan ya yi, wato cinye fatar dabbobi ba wai ganda kadai da ake samu daga kirgi ba, har ma fatun kananan dabbobi, musamman ma awaki da ake babbake su da fatunsu yayin da aka yanka su. Ga masu irin wannan al’ada, naman akuya bai amsa sunansa ba sai ya shiga tukunya hade da fatarsa. Duk wannan na nuni da yawan mutanen da ke cin ganda, wata girman kasuwar ganda a kasar nan. Hakan kuma ya zama manuniya ga dan kasuwa mai niyyar shiga harkar ganda, wato tabbacin kasuwarta da irin ribar da aka iya samu daga gare ta a matsayin daya daga cikin hanyoyi sarrafa fata da kirgi domin harkar kasuwanci.
Na yi bayanin yadda ake yin ganda a makon da ya gabata, da yadda za a adana ta da kuma kasuwarta. Yanzu kuma zan ci gaba da yi wa dan kasuwa bayanin yadda zai zabi fata da kirgi domin ya sayarwa masu bukata daban-daban, kamar masu yin ganda da majema na gargajiya da kamfanonin da ke jima irin ta zamani domin kayayyakin da za a yi amfani da su a nan gida Najeriya da kuma fata da kirgin da irin wadannan masana’antu za su sarrafa domin sayar wa kasashen duniya wadanda za su ci gaba da sarrafawa domin yin irin kayayyakin da suke bukata. Wani abu kuma da ban fada wa dan kasuwa ba a nan shi ne, Gwamnatin Tarayya ta dade da haramta fitar da danyar fata, wato fatar da ba a jeme ba.
Zan tashi daga nan idan Allah Ya kai mu makon gobe.