Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (4)
Kamar yadda na yi alkawari a makon jiya, a yau ne zan ci gaba da yi wa dan kasuwa bayanin yadda zai zabi fata da kirgi domin ya sayar wa masu bukata daban-daban, kamar masu yin ganda, da majema na gargajiya da kamfanonin da ke jima irin ta zamani domin kayayyakin da za a yi […]

Kamar yadda na yi alkawari a makon jiya, a yau ne zan ci gaba da yi wa dan kasuwa bayanin yadda zai zabi fata da kirgi domin ya sayar wa masu bukata daban-daban, kamar masu yin ganda, da majema na gargajiya da kamfanonin da ke jima irin ta zamani domin kayayyakin da za a yi amfani da su a nan gida Najeriya da kuma fata da kirgi da irin wadannan masana’antu za su sarrafa domin sayarwa kasashen duniya wadanda za su ci gaba da sarrafawa domin yin irin kayayyakin da su ke bukata.
Zaben fata da kirgi ya fara daga kyau da lafiyar dabbar da aka yanka. Kodayake ba lallai ne dan kasuwa ya ga dabbar da aka yanka ba kafin ya sayi fatarta ba, amma basirarsa za ta ba shi damar sanin cewa dabbar ko mai lafiya ce ko kuma a’a. Abin da ake gudu da fatar dabba marar lafiya shi ne, samun kurji (gyambo) ko tabo ko wata alamar cuta a jikin fata ko kirgin dabbar da za a saya. Wata nakasa kuma a jikin fata ko kirgi ita ce samun yanka a jikinta yayin da ake fede ta, walau daga ciki ko daga wajenta, ko ma ta kasance ta samu huda. To duk wannan ba zai hana dan kasuwa sayen fatar ba, sai dai kuma farashi zai bambanta; domin akwai mabukata kowane launin fata da kirgi, kama daga fata da kirgi masu lahani ya zuwa masu kyau gangariya. Wadannan mabukatan wadannan hajjoji mabanbanta za su biya farashi daban-daban daidai bukatarsu. dan kasuwa zai lura da cewa a yanzu ina magana ne a kan matakin farko na sayen fata da kirgi, inda dan kasuwa zai sayi fata ko kirgi daga hannun mahaucin da ya yanka dabbar da zai sayi fatarta ko kirginta. Wannan harka ta fata da kirgi tana da matakai kimanin uku ko ma fiye. Mataki na biyu na harkar shi ne, zama karami ko matsakaicin dila, wato mai sayen fata da kirgi daga hannun wadanda suka saya a matakin farko, ko kuma idan matsakaicin dila ne zai kasance zai saya a mataki na uku, wato ya saya daga hannun mutum na biyu a wannan rukuni, ma’ana, wanda ya saya daga hannun mutum na matakin farko. To abin lura dai ga dan kasuwa a kowanne mataki shi ne, lura da ka’idojin sayen fata da kirgi.
Abu na farko dai da dan kasuwa zai sani gama da harkar fata shi ne, fata da kirgi na da tsayayyen farashi a kowanne lokaci, wanda ke bambanta daga lokaci zuwa lokaci.
Kamfanoni masu sayen fata da kirgi domin sarrafa su a zamanance, wadanda har yanzu bayanina bai kai kan su ba, su ke tsayar da wannan farashi, su kuma suna amfani da farashin kasuwannin duniya wajen tsayar da wannan farashi domin suna fitar da wannan hajja bayan sun sarrafa ta, domin kamar yadda na furta a makon da ya gabata, Gwamnatin Tarayya ta dade da haramta fitar da danyar fata, wato fatar da ba a jeme ba, saboda haka wannan farashi na raguwa ne yayin da ya gangaro daga wadannan masana’antu ya zuwa manyan dilolin fata da kirgi, ya zuwa matsakaitan diloli da za su saya a daga wadanda suka saya a matakin farko da na biyu. Su ma ’yan kasuwa na wadannan matakan za su saita farashinsu daga wadannan diloli.
A kowanne mataki dan kasuwa zai shiga harkar fata da kirgi, akwai riba, sai dai dole sai ya yi amfani da basirarsa ta kasuwanci wajen samun ingantacciyar riba, musamman ma idan ya kasance zai shiga harkar a matakin farko da na biyu. Da bayani a kan irin wadannan basira da dabaru na sayen fata da kirgi a matakan farko da na biyu zan tashi idan Sarki Allah Ya kai mu makon gobe. Barka da Sallah.