Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (5)

Zan tashi da bayani a kan dabaru na sayen fata da kirgi a wannan makon, kamar yadda na yi alkawari a makon jiya. A makon na yau zan takaita wadannan dabaru a kan matakin farko na sayen fata da kirgi. Idan dan kasuwa na biye da ni, zai iya tunawa da wadannan matakai uku na […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (5)

Zan tashi da bayani a kan dabaru na sayen fata da kirgi a wannan makon, kamar yadda na yi alkawari a makon jiya. A makon na yau zan takaita wadannan dabaru a kan matakin farko na sayen fata da kirgi. Idan dan kasuwa na biye da ni, zai iya tunawa da wadannan matakai uku na sayen fata wadanda na yi batun su makonni biyu da su ka gabata, wato matakin farko da na harka matsakaiciya da kuma sayen fata daga manyan diloli domin sarrafa ta a masana’antu.
    Abubuwa guda shida suka kamata dan kasuwa ya lura da su yayin da zai shiga harkar fata da kirgi a matakin farko, su ne:
1.     Kyan fata da kirgi
2.     Farashin fata da kirgi
3.     Jarinsa
4.     Adanawa da sarrafa fata da kirgi
5.     Safarar fata da kirgi
6.     Babban dillalin da zai sayarwa fata
     A makon baya na yi wa dan kasuwa matashiyar cewa zaben fata da kirgi ya fara daga kyau da lafiyar dabbar da aka yanka; na ce kodayake ba lallai ba ne dan kasuwa ya ga dabbar da aka yanka kafin ya sayi fatarta ba, amma basirarsa za ta ba shi damar sanin cewa dabbar ko mai lafiya ce ko kuma a’a. Abin da ake gudu da fatar dabba marar lafiya shi ne, samun kurji (gyambo) ko tabo ko wata alamar cuta a jikin fata ko kirgin dabbar da za a saya. Na kuma kara da cewa, wata nakasa kuma a jikin fata ko kirgi ita ce samun yanka a jikinta yayin da ake fede ta, walau daga ciki ko daga wajenta, koma ta kasance ta samu huda. Wani abu kuma da na shafa’a ban sanar da dan kasuwa a wancan makon ba, shi ne ya tabbatar fatar ba ta wari, wato sabuwa ce dabbar da aka yanka a wannan ranar ba kwananniya ba ce.
    Kamar kuma yadda na furta a makon na jiya cewa duk wadannan lahani fata da kirgi ba za su hana dan kasuwa sayen fatar ko kirgin ba, sai dai kuma zai saye su da halinsu, wato farashi zai bambanta; domin akwai mabukata kowanne launin fata da kirgi, kama daga fata da kirgi masu lahani ya zuwa masu kyau gangariya.     
    To a nan zan shiga zango na biyu na dabarun sayen fata da kirgi, wato inda zan yi bayani a kan farashi, wanda ya yi harshen damo: wato farashin saye da farashin sayarwa. A kullu-yaumin dan kasuwa zai kaddara cewa zai sayar da duk fatar da ya saya ga wani babban dillalin fata, wanda komai dare, komai rana zai kai masa fata da kirgin da ya saya, shi kuma zai saya ya biya shi kudinsa. To abin lura a nan ga dan kasuwa mai sayen fata a matakin farko shi ne, wannan babban dillali na da tsayayyan farashi a kowanne mako. Ba wai lallai ne wannan farashi ya bambanta ba a kowanne mako ba, amma duk sa’in da farashin fata ko na kirgi ko ma duk na guda biyun suka canja, wannan babban dillali zai sanar da ’yan kasuwa da ke kawo masa fata da kirgi ya saya. Saboda haka da wannan tsayayyan farashi a zuciyarsa ne dan kasuwa zai nufi neman fata da kirgi.
    Saboda haka, dan kasuwa zai yi nazarin wahalhalun da zai yi wa fata da kirgin da ya saya kafin ya kai wa wannan dillalin, inda zai cire su daga farashin da zai sayi fatar, sannan ya kuma yi wa ribar da yake sa ran samu gurbi. Wani abu kuma da zai yi la’akari da shi wajen sayen fata da kirgi shi ne, wanda zai sayarwa da hajjarsa zai yi amfani da sikeli ya auna ya biya shi; wato babban dillali na amfani da ma’auni ne ba sayen daidai yake ba. Shi kuwa karamin dan kasuwa mai saye a matakin farko da daidai- da-daidai yake saye, kuma a yawancin yanayi ba ya amfani da sikeli wajen sayen wannan hajja. Amma akan samu wasu sukan rike karamin sikeli na hannu su na yawo da shi domin auna hajjar da za su saya. To a nan basira da dabara za ta yi wa dan kasuwa amfani a kan cinikinsa. Zan ci gaba daga nan idan Allah Ya kai mu makon gobe.