Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (6)

A yau zan shiga zango na uku na dabarun sayen fata da kirgi. Idan mai karatu na biye da ni zai iya tuna cewa na tsaya a kan farashin fata da kirgi, wato har da kayyadadden farashin wadannan kayayyaki daga kamfanonin da ke sayen su zai yi wa karamin dan kasuwa jagora wajen sayen fata […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (6)
Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (6)

A yau zan shiga zango na uku na dabarun sayen fata da kirgi. Idan mai karatu na biye da ni zai iya tuna cewa na tsaya a kan farashin fata da kirgi, wato har da kayyadadden farashin wadannan kayayyaki daga kamfanonin da ke sayen su zai yi wa karamin dan kasuwa jagora wajen sayen fata da kirgi daga hannun wadanda suka samar da su, domin ya fitar da wahalhalun da ya yi wa kayan, shi ma ya samu riba mai tsoka. Kamar yadda na yi bayani a zango na biyu a makon da ya gabata, na yi bayanin farashi biyu tsakanin wadanda dan kasuwa zai fitar da wahalhalun da ya yi wa kayan da saya, ya kuma samu riba, wato tsayayyan farashin da zai sayar wa babban dillalin fata da kirgi da kuma farashin da zai saya daga hannun masu samar da fata da kirgi. 

To, dan kasuwa zai iya amfani da basirar da Allah ya ba shi ya dadaita farashin da zai sayi fata da kirgi daga hannun masu shi domin ya fitar da tasa ribar, tun da farashin da zai sayar tsayayye ne. Mai karatu zai lura ina ta maimaita wannan kudiri, amma idan ya lura da kyau zai ga cewa wannan tsarin farashi na fata da kirgi ya bambanta da na sauran harkar kasuwanci, inda farashin da dan kasuwa ya sayi kaya ke kasancewa tsayayye a mafi yawanci lokuta, sannan ya saka tasa ribar domin fitar da farashin da sayar da hajjarsa. To harkar fata da kirgi sabanin haka ce, wato tsayayyan farashin da dan kasuwa zai sayar da hajarsa, shi zai ba shi hasken yadda zai saye ta.
Idan kuma mai karatu na biye da ni, zai iya tunawa da maganar da na yi a makon da ya gabata, inda na bayani a kan kyan fata da kirgi, inda na ce dan kasuwa zai iya sayen fata ko kirgi ba lallai mai kyau ba a bisa ka’idojin da na zayyana na kyan fata da kirgi a makon shekaranjiya. Ita dai fata mai kyau ita ce wacce dan kasuwa zai saya domin ya kai masana’anta. Ana cewa wannan hajja giredi ce. To ko da dan kasuwa ya samu fata ko kirgi da lahani, wato ba ta cancanci ya kai ta masana’anta ba, zai iya sayen ta domin sayarwa masu yin ganda ko majeman gargajiya. Ana kiran wannan hajja ‘Zare’, ko ‘Dameji’. dan kasuwa zai sayi wannan fata ko kirgi a kan farashi mai sauki, domin masu sayen ta a hannunsa ba za su ba shi farashin fata mai kyau ba.
Shawara a nan ita ce, dole dan kasuwa mai sayen fata da kirgi ya mayar da hankali wajen sayen giredin fata ya kuma san yadda zai daidaita farashinsa, kamar yadda na yi a makalar makon baya na kuma kara bayani a wannan makon. In kuma mai karatu zai tuna na yi batun ’yan kasuwar fata da kirgi da ke yawo da karamin sikeli na hannu, wato a makon jiya ke nan, domin auna hajar da za su saya. Irin wadannan ’yan kasuwa sun riga sun tsayar da nasu farashin tun kafin su fito daga gida, saboda haka sun san ko nawa za su biya kowanne kilo na fata ko kirgi. Wasu lokutan ma za su fada wa wadanda za su sayi kayan a wurinsu farashin da suka tsayar domin sayen kayansu, kuma da wuya su gusa daga hakan.
Idan dan kasuwa ya dage da sayen fata da kirgi masu kyau, zai rika sayen zaren fata da kirgi daidai gwargwado, domin ribar su kadan ce, ko kasuwarsu ba tsayayyiya ba ce. Wannan zai hana shi daure jarinsa a zaren fata ba.
Idan Allah Ya kai mu makon gobe zan tashi daga aji na uku daga shida da na zayyana a makon jiya, wato jarin dan kasuwa.