Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (7)
Zan yi bayani a kan jarin dan kasuwa a matsayin abu na uku daga cikin jerin abubuwa guda shida da na lissafa a makon shekaranjiya a matsayin dabarun sayen fata da kirgi, wadanda suka kamata dan kasuwa ya lura da su yayin da zai shiga harkar fata da kirgi a matakin farko. Idan mai karatu […]

Zan yi bayani a kan jarin dan kasuwa a matsayin abu na uku daga cikin jerin abubuwa guda shida da na lissafa a makon shekaranjiya a matsayin dabarun sayen fata da kirgi, wadanda suka kamata dan kasuwa ya lura da su yayin da zai shiga harkar fata da kirgi a matakin farko. Idan mai karatu na biye da ni, zai iya tuna su kamar haka: Kyan fata da kirgi; Farashin fata da kirgi; Jarin dan kasuwa; Adanawa da sarrafa fata da kirgi; Safarar fata da kirgi da kuma Babban dillalin da zai sayar wa fata da kirgin da ya saya.
Na yi bayanin dabara ta daya da ta biyu a makalun makonnin baya, wato Kyan fata da kirgi da kuma Farashin fata da kirgi. A game da jarin dan kasuwa kuwa, harkar fata da kirgi ba ta bukatar jari mai yawa domin fara ta. Jarin da dan kasuwa zai nema domin fara wannan harka ya danganta da kusantarsa da kasuwar da zai sayi hajjarsa, da kuma babban dillalin da zai sayarwa da hajjarsa. Wato idan inda dan kasuwa zai sayi fata da kirgi kusa da shi ne, kuma dillalin da zai sayarwa shi ma kusa da shi ne, to ba zai bukaci jari mai yawa ba; yana iya farawa da kimanin jarin Naira dubu biyar. Sannan idan kasuwar da zai sayi wannan hajja tana kusa da shi, misali a garinsu take, amma dillalin da zai sayarwa yana wani gari daban, to dan kasuwa sai ya bukaci jarin da ya fi na dan kasuwar da ya kasance kusa da kasuwar da zai sayi hajjarsa, kuma kusa da dillalin da zai sayarwa.
Wannan dan kasuwa zai iya tashi da safe ya tafi mayanka (ko kwata) ya sayi fata ko kirgi na iya jarinsa, ya kasance ya kai wa dillalin da zai saya daga gare shi ya zuwa da rana ko yammacin wannan ranar. Wannan dan kasuwa ba ya bukatar ya nemi wuri ya tara fata da kirgin da ya saya, ya kuma nemi sinadarin adana wannan hajja. Ba kuma zai nemi motar da zai debi hajar ya zuba domin kai wa dillalin ba. Yana iya dibar hajarsa a hannu, ko a kan babur ko cikin tasi ya kai wa dillalin da zai saya. Duk wannan ya danganta da yawan fata da kirgi da ya saya.
Shi kuwa dan kasuwar da kasuwarsa to fata da kirgi tana kusa da shi, amma dillalinsa na nesa, kamar yadda na misallta a baya, to dole ya kasance ya sayi fata da kirgi da yawa ya tara kafin ya yi yunkurin kaiwa dillalinsa, domin ba zai kasance yana biyan kudin mota a kullum yana kai hajja kalilan ba. Wannan zai rage masa riba kwarai da gaske, koma ya yi asara. Wato irin wannan yanayi ya kasance sai dan kasuwa ya nemi wurin ajiye fata da kirgin da ya saya, sannan sai ya tanadi sinadarin da zai adana su da shi, tun da ba ranar da ya sayi wannan hajja zai kai ta ga mai sayenta ba. Kuma dole sai dan kasuwa ya nemi motar da za ta kwashe wannan hajar idan ya tara domin kai ta ga dillalin da zai saya. Wato dole sai ya tanadi jarin da ya fi na dan kasuwa na baya.
A bisa shawara wannan dan kasuwa na bukatar akalla Naira dubu 50 ko fiye domin tafiyar da harkarsa; kuma wannan jarin ya danganta da samuwar hajar a kusawar ta kusa da shi, da kuma kusancin garin da yake da garin da dillalin da zai kai wa wannan hajar. Zan yi karin bayani a kan wannan, sannan kuma in yi bayani a kan dan kasuwar da zai kasance kasuwar da zai sayi hajjarsa da kuma dillalin da zai sayarwa hajarsa, ba a gari daya suke ba, duk wannan sai Allah Ya kai mu makon gobe.