Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (8)

A wannan makon zan karasa bayani a kan jarin dan kasuwa a matsayin abu na uku daga cikin jerin abubuwa shida da na lissafa a makonnin baya. Sannan kuma in shiga basirar sayen fata da kirgi ta hudu, wato Adanawa da Sarrafa Fata da kirgi. Idan mai karatu bai manta ba na tattauna irin wadannan […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (8)

A wannan makon zan karasa bayani a kan jarin dan kasuwa a matsayin abu na uku daga cikin jerin abubuwa shida da na lissafa a makonnin baya. Sannan kuma in shiga basirar sayen fata da kirgi ta hudu, wato Adanawa da Sarrafa Fata da kirgi.

Idan mai karatu bai manta ba na tattauna irin wadannan dabarun sayen fata da kirgin guda biyu a baya kafin in kawo kan jarin dan kasuwa a matsayin dabara ta uku, su ne: Kyan fata da kirgi da kuma Farashin fata da kirgi, wadanda suka kamata dan kasuwa ya lura da su yayin da zai shiga harkar fata da kirgi a matakin farko. Basira ta biyar da ta shida kuwa su ne Safarar fata da kirgi da kuma, Babban dillalin da zai sayar wa fata da kirgin da ya saya.
A tattauna jarin dan kasuwa a matsayin basirar sayen fata da kirgi a matakin farko na wannan harka da na yi a makon jiya, na tsaya a kan yadda dan kasuwar da kasuwarsa ta fata da kirgi tana kusa da shi, amma dillalinsa na nesa. Na bai wa irin wannan dan kasuwa shawarar yadda zai sayi hajarsa da kuma irin karfin jarin da zai nema domin shiga wannan harka ta saye da sayar da fata da kirgi. Kafin nan, a makon shekaranjiya na yi bayanin yanayin da dan kasuwa zai kasance kasuwar sayen hajarsa da dillalin da ke sayen hajar tasa duk suna kusa da shi. A nan ma na ba irin wannan dan kasuwa shawarar yadda zai tafiyar da wannan harka domin samun alherin da ke cikinta, da kuma irin jarin da yake bukata domin tafiyar da ita.
A wannan makon kuwa zan shawarci dan kasuwar da ya kasance kasuwar da zai sayi kayansa da kuma dillalin da zai sayar wa wannan kaya dukkansu suna nesa da shi. Irin wannan dan kasuwa na iya kasancewa ba zai iya sayen fata da kirgi daga kasuwarsa mai nisa a rana daya ba, har ya zo a ranar ya kuma kai ta ga mai saye a rana daya. A wasu lokuta kuma, irin wadannan ’yan kasuwa na iya kasancewa suna sayo hajarsu daga kasuwanni daban-daban su tara kafin a kai hajar ga dillali. Abu na farko da za a lura a nan shi ne akwai bukatar wannan haja ta kwana, ko ma ta samu kwanaki a hannun dan kasuwa kafin ya kai wa dillali, sabanin yanayi na biyu da na yi bayani baya, inda hajar za ta isa ga babban dillali a rana daya.
Wannan yanayi na bukatar wurin ajiya da dan kasuwa zai ajiye wannan hajar kafin ya kai ta ga mai saye, sannan akwai bukatar adani kafin ya kai ta ga mai sayen, domin kada ta lalace. Fata da kirgi na iya lalacewa awanni kadan bayan an samar da ita, wato bayan fede dabbar an sayar wa dan kasuwa fatar ko kirgin. Za a kuma iya lura cewa mahautan da ke samar da wannan haja na sayar da ita da zarar an samar da ita, domin gudun lalacewar ta, ko kuma kada a yi hidimar adanata, wanda zai bata lokaci ya kuma rage ribar da za a iya samu.
Ina shawartar dan kasuwa a nan da ya nazarci mai irin wannan harkar, kuma wanda ke a irin wannan yanayin da zai ajiye fata da kirgi a hannunsa su kwana ko ma su samu kwanaki kafin ya kai wa mai saye. Wannan zai ba shi hasken yadda zai sarrafa ta yayin da take hannunsa. Kuma akwai bukatar irin wannan dan kasuwa ya san yadda zai daidaita farashinsa na saye, inda zai fitar da wahalhalun sufuri da na sarrafawa. Zan bayar da cikakken bayani a kan sarrafa fata da kirgi a matsayin mataki na hudu na dabarun samun nasarar harkar fata da kirgi.