Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (9)

Zan bayar da cikakken bayani a kan adanawa da sarrafa fata da kirgi a matsayin mataki na hudu na dabarun samun nasarar harkar fata da kirgi a wannan makon. Mai karatu zai iya tuna irin wadannan dabaru uku da na yi bayaninsu a baya, wato Kyan fata da kirgi da Farashin fata da kirgi da […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Fata da kirgi (9)

Zan bayar da cikakken bayani a kan adanawa da sarrafa fata da kirgi a matsayin mataki na hudu na dabarun samun nasarar harkar fata da kirgi a wannan makon. Mai karatu zai iya tuna irin wadannan dabaru uku da na yi bayaninsu a baya, wato Kyan fata da kirgi da Farashin fata da kirgi da kuma Jarin dan kasuwa mai irin wannan harka. Sauran dabarun da suka kamata ya lura da su yayin da zai shiga harkar fata da kirgi a matakin farko su ne: Safarar fata da kirgi da kuma Babban dillalin da zai sayar wa fata da kirgin da ya saya.

A makon jiya na yi bayanin yadda dan kasuwa zai kai kayansa kasuwa da kuma dillalin da zai sayar wa wadannan kaya dukkansu na nesa da shi. Irin wannan yana iya kasancewa ba zai iya sayen fata da kirgi daga kasuwarsa mai nisa a rana daya ba, har ya zo a ranar ya kuma kai ta ga mai saye a ranar ba. A wasu lokuta kuma, irin wadannan ’yan kasuwa na iya kasancewa suna sayo hajarsu daga kasuwanni daban-daban su tara kafin a kai hajar ga dillali. Abu na farko da za a lura a nan shi ne, akwai bukatar wannan haja ta kwana, ko ma ta samu kwanaki a hannun dan kasuwa kafin ya kai wa dillali, sabanin yanayi na biyu da na yi bayani a baya, inda hajar za ta isa ga babban dillali a wannan ranar.
Wannan dalili ne ya sa dole dan kasuwa ya adana ya kuma sarrafa fata da kirgin da ya saya, domin kada su lalace. To babban abun lura a nan shi ne, wannan adanawa da sarrafawa da zai yi wa hajarsa zai kara mata kudi a kan abin da ya sayo ta; wannan zai rage masa riba ko ma ya sa shi asara idan farashin da zai sayar da ita ya kasa farashin da ya saye ta. Kuma kada mai karatu ya manta tsokacin da na yi a makklar baya cewa, wannan harka sabanin sauran ce, saboda dan kasuwa ya san tsayayyan farashin da zai sayar da hajar da zai saya, amma babbar basirarsa ta ya samu riba mai inganci ita ce, ya yi kokarin sayen hajar kasa da wannan tsayayyen farashin.
Kuma adanawa da sarrafa fata da kirgi za su fadada girman jarin dan kasuwan da zai shiga wannan harkar a matakin farko. Adana fata da kirgi na bukatar wani wuri na musamman da zai kebe domin yin hakan. Fata da kirgi na fara yin kimanin awa biyar bayan cire su daga jikin dabbobin da aka fitar da su, saboda haka duk inda suka kwana za su yi warin da zai damu jama ‘a. Ya zama dole mai wannan harka ya tanadi wurin da zai adana hajarsa kafin ya kai ta kasuwa. Wani abu kuma da zai yi la’akari da shi a nan shi ne, fata da kirgi nama ne, saboda haka dole ya dauki matakan da zai kare su daga dabbobin gida irin su kare da mage da beraye.
Fata da kirgi na kuma iya lalacewa idan aka bar su suka kai wani lokaci ba a sarrafa su ba. Sarrafawa a wannan matsayi na matakin farko shi ne a yayyafa mata abin da ake kira gishirin jima a cikinta. dan kasuwa zai bukaci wuri, musamman ma kabgo inda zai baje kowace fata da kirgi, inda zai sa bangaren da yake da gashi a kasa domin cikin ya kalli sama. Zai barbada gishirin a cikin fatar ko kirgin. Wannan zai rage musu wari ya kuma hana su rubewa kafin ya kai su ga babban dillalin da zai sayarwa. Idan ba a manta ba a wata makala a baya na shawarci dan kasuwa mai niyyar shiga wannan harkar da ya nemi shawarar wadanda ya tarar a cikinta. A wannan karon ma zan bukaci ya nemi shawarar kwararru, wato Malaman Fata (wadanda zan yi magana a kansu gaba), ko kuma ’yan kasuwa da ke cikin wannan harkar a kan sarrafa fata da kirgi.