Sarrafa Albarkatun Gona: Gawayi
A shimfidar da na yi a kan albarkatun gona, kafin in fara makalolin da suka shafi haka a wannan filin kimanin wata hudu da suka gabata, na yi bayanin cewa albarkatun gona sun hada dabbobi da dukkan albarkatun daji masu amfani wajen bunkasa arziki da jin dadin al’umma. Na yi makalu a baya a kan […]

A shimfidar da na yi a kan albarkatun gona, kafin in fara makalolin da suka shafi haka a wannan filin kimanin wata hudu da suka gabata, na yi bayanin cewa albarkatun gona sun hada dabbobi da dukkan albarkatun daji masu amfani wajen bunkasa arziki da jin dadin al’umma. Na yi makalu a baya a kan karo da man kade da ake samu daga kadanya da dai makamantansu. A wannan makon zan yi makala a kan gawayi.
Na yi tsammanin mutanen karkara da yawa za su yi mamaki idan suka ga makala a kan gawayi, yayin da na samu wata wasika ta yanar gizo daga wani mai karatu a garin Jos, kimanin wata uku da suka gabata, yake neman in yi makala a kan harkar gawayi. Harkar gawayi a biranen kasar nan ba bakuwa ba ce, domin iyali da dama sun maye murahunsu na itace da na kananzir ya zuwa na gawayi a cikin shekarun nan da farashin kananzir ya tashi.
Haka kuma, fasahar yin murhun gawayi da ta samu kimanin shekara goma baya, ta sa amfani da gawayi a matsayin makamashin girki ta inganta, saboda haka amfani da gawayi ya bazu daga manyan birane da garuruwan kasar nan ya zuwa wasu sassa na karkara.
Har yanzu dai wasu masu karatu da ke zaune a karkara da ba su fuskanci irin gawayin da zan yi bayani a kai ba, za su yi mamaki, domin a gare su gawayi wani abu ne da ake samu yayin da aka kona itace, ya ci wuta ya cinye ya bar shi da sauran toka.
Ga irin wadannan mutane, amfanin gawayi bai wuce a saka a cikin dutsen guga ba, ko kuma a cikin kasko domin yin turaren wuta ba, ko kuma a dumama daki lokacin sanyi. Amma mazauna alkarya sun san akwai gawayi na musamman da wasu ke kira ‘kwal’ da ake amfani da shi wajen makamashi domin yin girki da sana’oí irin su kira da gasa burodi a sassa daban-daban na kasar nan.
Wani abu da zai kara ba wanda bai san wannan gawayin ba mamaki shi ne, wannan gawayin na cikin manyan albarkatun kasa a Najeriya wadanda ba su jibanci man fetur ba, da ake bukata a da yawa daga cikin manyan kasashen duniya. Ana samar da irin wannan gawayi daga wasu itace masu nagarta da ake samu a jihohin Kaduna (musamman ma kudancin Kaduna) da Filato da Nasarawa da Binuwai da Neja da Kogi da Kwara, dukkanin su a yankin Arewacin Najeriya. A kudancin kasar nan kuwa, ana samun gawayin a jihohin Oyo da Ogun da Ekiti da Ondo. Idan mai karatu ya lura zai ga ana samun wadannan itatuwa a jihohin tsakiyar Najeriya da na yammacin kasar, inda ake da yalwar ruwan sama, fiye da na sauran shiyyoyin Arewa maso Gabas da na Arewa maso Yamma.
Wadannan itatuwa na jure wa wuta domin su kan dauki tsawon kwanaki suna cin wuta, kafin wutar ta mutu a samu gawayin, kuma akwai wata fasaha da ake amfani da ita wajen kona itacen domin samar da gawayin. Wannan fasaha, da kuma ingancin itacen da yadda ake sarrafa shi, ya sa wannan gawayi ba ya fitar da hayaki, ba ya kuma saurin konewa kamar gawayin da aka samar daga itatuwanmu na shiyyar Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma. Gawayin kuma na da saurin kama wuta idan an kunna shi, yana kuma dadewa yana ci, ya bayar da wuta mai zafin gaske.
Zan tattauna harkar gawayi a ciki da wajen kasar nan, in kuma ba dan kasuwa yadda zai samu wannan haja a kasar nan da yadda zai sarrafa ta domin sayarwa a kasuwanninmu na gida da kasuwannin kasashen ketare, idan Allah Ya kai mu makon gobe.