Sarrafa Albarkatun Gona: Gawayi (2)

Zan dora daga inda na tsaya a kan saye da sayar da gawayi a kasuwanninmu na gida da na waje. Na yi shimfida a kan wannan harka a makon jiya, a matsayinta na daya daga cikin batutuwan da na yi kusan watanni hudu ina makala a kai, wato harkokin sarrafa albarkatun gona (da na gandun […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Gawayi (2)
Sarrafa Albarkatun Gona: Gawayi (2)

GawayiZan dora daga inda na tsaya a kan saye da sayar da gawayi a kasuwanninmu na gida da na waje. Na yi shimfida a kan wannan harka a makon jiya, a matsayinta na daya daga cikin batutuwan da na yi kusan watanni hudu ina makala a kai, wato harkokin sarrafa albarkatun gona (da na gandun daji) domin kasuwannin Najeriya da na kasashen ketare, domin bunkasa arziki da jin dadin al’umma.
Na yi bayanin irin wannan gawayi a makon da ya gabata, na kuma lasafta amfaninsa ga al’ummar kasar nan da kuma farin jininsa a kasashen ketare. Na kuma yi bayanin jihohin da ake samunsa a kasar nan irin su Kaduna (musamman ma kudancin Kaduna) da Filato da Nasarawa da Binuwai da Neja da Kogi da Kwara, dukkansu a yankin Arewacin Najeriya. A kudancin kasar nan kuwa, ana samun gawayin a jihohin Oyo da Ogun da Ekiti da Ondo.
 A makalar makon jiya, na yi bayanin cewa ana samar da irin wannan gawayi daga wasu itace masu nagarta da ake samu a cikin wadannan jihohin. To na samu wasiku da yawa ta kafar sadarwar intanet game da makalar, inda aka yi mini tambayayoyi masu yawa game da gawayi, wanda a ciki akwai tambayar yadda ake yin wannan gawayin. Tun da wannan shafi na kasuwanci ne, ba na koyar da sana’o’i ba, hakkina a nan in yi bayanin yadda za a sayi hajja a sayar da ita, wannan ya hada yadda za a kara mata (ko sarrafa ta) wata martaba a kai ta kasuwa a sayar da ita. Misali, zan iya bayanin wuri da yadda dan kasuwa zai sayi gawayi ya sarrafa shi ya kai wata kasuwa a nan cikin Najeriya ko a kasashen ketare ya sayar. Duk da haka, ana samar da wannan gawayi ne daga kona wadannan itatuwa a cikin wani kebabben yanayi da ake kira ‘Pyrolysis’ da Turanci. Ana kona itacen ta wannan hanyar ganga-ganga, ba tare da iska ba.     
Wannan tsari na yin gawayi na da injinan yinsa, akwai kuma tsohon tsari da turawan mulkin mallaka suka zo na yin wannan gawayi da har yanzu ana amfani da ita a kasar nan.  Harkar gawayi ta dan ci baya a kasar yayin da harkar jirgin kasa ta durkushe a kasar nan, saboda mafiyawan cin wuraren da ake samun wannan gawayi na kusa da tasoshin jirgin kasa. Ta wannan kafar sufuri ne ake jigilar gawayin a cikin kasar, har ya zuwa manyan garuruwan arewacin kasar nan. Ita kuwa kasuwar kasashen waje na samun gawayin ne daga Najeriya ta cikin teku, wato ta jirgin ruwa saboda nauyinsa.
     Gawayin Najeriya na da farin jini a kasuwannin duniya kamar yadda na yi bayani a makon baya. Ana sayen gawayin Najeriya a kasar Amurka da kasashen Majalisar Turai (European Union) da wasu kasashen Nahiyar Asiya. Tan din gawayi a wadannan kasuwanni na kamawa daga Yuro (Euro) 200 ya zuwa Yuro 250, wato daga kimanin Naira dubu 60 ya zuwa Naira dubu 75; wannan ya danganta da kyawun gawayin da kuma a irin mazubin da aka saka shi. A nan kuwa Najeriya, farashin Tan din gawayi na kamawa daga Naira dubu 18 ya zuwa dubu 25, farashin ya danganta da wurin da aka saya da kyawun gawayin da kuma lokacin da aka sayi gawayin.
     Zan yi bayani a kan kasuwar gawayi a ciki da wajen kasar nan idan Allah Ya kai mu makon gobe.