Sarrafa Albarkatun Gona: Gawayi (3)
A makon da ya gabata na yi alkawarin yin bayani a kan kasuwar gawayi a ciki da wajen kasar nan a makalar wannan makon. Kamar yadda na yi bayani a kasidar farko, kasuwar gawayi a garuruwa da biranen kasar nan a bude take, musamman ma yanzu da sufurin jirgin kasa ke kokarin inganta a kasar […]

A makon da ya gabata na yi alkawarin yin bayani a kan kasuwar gawayi a ciki da wajen kasar nan a makalar wannan makon. Kamar yadda na yi bayani a kasidar farko, kasuwar gawayi a garuruwa da biranen kasar nan a bude take, musamman ma yanzu da sufurin jirgin kasa ke kokarin inganta a kasar nan, wanda gurguncewarsa ta yi wa harkar rauni a arewacin kasar nan. Ana sayar da gawayin a buhuhuna ga manyan dillalai a wurare daban-daban a wadannan garuruwa da birane, su kuma kananan ’yan kasuwa masu yin wannan harka na sayen buhuhunan daidai karfinsu su kasa a kwanuka da sauran mazubai domin amfanin masu bukata.
Masu sarin gawayi na samunsa a garin Minna da sauran kauyukan da ke zagaye da garin, da garuruwan kudancin garin Kaduna da suka shafi lardin da ake kira ‘Forest’ da makwabtansa da ke Jihar Nasarawa, musamman ma tsakanin Keffi da Lafiya; sai kuma garuruwan da ke tsakanin Lafiya da Jos. Sauran wuraren da ake samun gawayi a Arewa kuma sun hada sashen tsohuwar Jihar Kwara da ta hada da jihar kwara ta yanzu da wani sashe na Jihar Kogi. Wadannan garuruwa sun hada da Jebba da Egbe da Kabba da Omu Aran. A shiyyar yammacin kasar nan kuwa ana samun gawayin a Ogbomoso da Oyo da Isheyin da Saki Igbo-Ora.
’Yan kasuwa masu sarin gawayi na samunsa a cikin buhuhuna da sauran mazubai iri-iri masu girma daban-daban. Farashin gawayi a wadannan wurare na tafiya da farashin gawayi a kasuwannin duniya a mafi yawancin lokaci. Misali, kasuwar gawayi ta kasashen da ke Nahiyar Turai na ci tsakanin watan Mayu zuwa watan Agusta, musamman ma kasashen nahiyar da ke sayen gawayi daga Najeriya, irin su Denmark da Faransa da Belgium da Holland da Ingila da Jamus. Kamfanoni da ’yan kasuwa daga wadannan kasashe na fara bayar da odar gawayin tun daga watan Satumba, ya zuwa watan Janairu na kowace shekara. Su kuwa kasashen da ke Nahiyar Asiya, irin su Kuwait, wadanda ke sayen gawayi daga Najeriya, suna saye ne a kowanne wata a cikin shekara. Saboda haka farashin gawayi na tashi daga tsakanin a kasuwannin duniya tsakanin watan Nuwamba ya zuwa watan Janairu, wannan shi ne lokacin da masu sayen gawayi domin sayarwa a kasashen ketare ke saye a Najeriya, kuma shi ne lokacin da gawayin ke tsada a wuraren da ake sarar da shi a Najeriya.
Babbar matsalar harkar gawayi ga mai sayen sa da yawa, musamman ma wanda zai fitar da shi zuwa kasashen ketare, ita ce, gawayi ba abin da za ka saya ka ajiye ba ne, saboda mamaye sarari da yake yi. Kuma shi gawayi wata hajja ce da ba za ka saya ka ajiye ka jira oda daga abokan hulda daga kasashen waje ba, saboda ba za ka san irin bukatarsu ba, sai sun ba ka odar za ka san irin wanda suke so, a kuma wane irin mazubi suke bukatarsa. Wannan ya sa idan aka bayar da oda za ka ga kasuwa ta cunkushe, farashi ya tashi, wani lokacin ma kayan su yi kadan. Wannan yanayi ya sa dan kasuwa sai ya hada da dabara wajen saye da sayar da gawayi a cikin kasa da kuma a kasuwannin duniya. Irin wadannan dabaru ne zan yi bayani a kai idan Allah Ya kai mu makon gobe.