Sarrafa Albarkatun Gona: Gawayi (5)

A wannan makon ne zan yi zangon karshe a kan makalar gawayi. Idan mai karatu na biye da ni, a makon jiya ne na yi alkawari zan duba dabarar sayen gawayi, domin sayarwa a kasuwannin kasashen ketare. A makalar ta baya, na yi batun yadda wasu ’yan kasuwar da suka dade cikin harkarsu kan bai […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Gawayi (5)
Sarrafa Albarkatun Gona: Gawayi (5)

A wannan makon ne zan yi zangon karshe a kan makalar gawayi. Idan mai karatu na biye da ni, a makon jiya ne na yi alkawari zan duba dabarar sayen gawayi, domin sayarwa a kasuwannin kasashen ketare. A makalar ta baya, na yi batun yadda wasu ’yan kasuwar da suka dade cikin harkarsu kan bai wa masu yin gawayi adibas na kudi, domin tanadar musu gawayin a wani lokacin da suke bukata. To wannan ba dabara ba ce ga sabon mai shiga harkar gawayi, tun da ba shi da kyakkyawar fahimtar kasuwar gawayi. Tsofaffin masu wannan harka na da masaniyar kasuwar gawayi a gida Najeriya da kasashen ketare. Misali sun san har da farashi ya kasance kimanin shekaru uku zuwa biyar da suka shude, kuma suna da hasken manuniyar yadda kasuwar za ta iya kasancewa a shekara daya ko biyu masu zuwa. Saboda haka zai kasance yana da tsayayyun alkalumma da zai iya yin yarjejeniya da mai yin gawayin, wacce za ta amfane shi a kasuwance.
Irin wadannan tsofaffin masu harkar gawayi na da tabbacin samun oda daga abokan huldarsu daga kasashen ketare. Idan mai karatu bai manta ba, na ja hankalinsa a kan kada ya fara sayen gawayin da zai sayar a kasashen ketare har sai ya samu oda daga wanda, ko wadanda za su sayarwa gawayin, domin a kan samu sabanin bukatar irin gawayin da masu saye ke so. Kuma gawayi na da mamaye wurin ajiya saboda yawansa, inda a alkarya ake bukatar kama masa hayar ma’ajiyi, a kashe kudi mai yawa.      
Ana samun gawayi a buhhuunan leda masu alamar ‘L’ wato manya, inda za a sau an cika su sun yi tsiri an dinke. dan kasuwa zai taya farashin gawayi ya yi kyakkyawan bincike kafin ya fara saye. dan kasuwa zai kuma samu gawayin a zube a wurin manyan masu yinsa, inda za a nemi ya saye shi ba tare da an dura ba, ko kuma a yi amfani da sikeli wajen sayar masa a kan wani farashin kilo da mai saye da mai sayarwa za su amince da shi. Saboda haka, basirarsa ta farashin buhu da binciken kasuwa da ya yi ita ce za ta taimaka masa idan ya yarda ya yi cinikin ta wannan kafar. Dadin wannan tsarin shi ne, dan kasuwa zai ga gawayin zahirinsa ba tare da boye wani ha’inci a cikinsa ba.
Idan dan kasuwa ya amince da sayen gawayin da ke cikin buhu, to na farko dai sai ya tabbatar da cewar gawayin irin wanda yake bukata ne, wato wanda aka ba shi oda ne. Zai tabbatar da haka ne ta daukar samfurin wadannan buhuhunan, ya farke shi domin tabbatar da kasancewarsa irin wanda yake bukata ne, kuma mai tsabta.
Ko ma yaya dan kasuwa ya sayi gawayinsa, akwai tsarin mazubi da abokan huldarsa ke bukatar a aika musu da gawayin; wasu na bukatar gawayin ne a cikin buhuhuna masu nauyi daban-daban, kama daga kilo uku ya zuwa kilo 15. Wasu kuma na bukatar a zuba musu gawayin a budaddun manyan mazubai masu tsayin kimanin kafa 40. Irin wadannan manyan mazubai na cin gawayi fiye da tan 20.
Kasuwar gawayi a kasashen duniya kullum habaka take, musamman ma a kasashen Turai, saboda kwarjininsa wajen rashin gurbata mahalli in an daidai ta shi da sauran makamashin da ake samarwa daga gurbataccen man fetur. kasar Birtaniya kawai na amfani da fiye da tan dubu 60 na gawayi, kiyasin da ya fi yawan gawayin da ake fitarwa daga Najeriya.  Gwamnatin Tarayya kuma na tallafa wa wannan harka domin inganta hanyoyin samun kudin shiga daga kasashen ketare, wadanda ba su danganci man fetur ba. Tallafin na zuwa ta fanni lamanin fadada jarin fitar da haja waje, wato, ‘Edport Edpansion Grant’ da kuma Takardar Shaidar Lamani ta ‘Negotiable credit certificate (NDCCS)’