Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada
A wannan makon zan fara bayanin yadda dan kasuwa zai sarrafa gyada domin sayarwa a kasuwanninmu na gida da na waje. Ita dai gyada ba ta bukatar gabatarwa ga duk wani mazaunin kasar nan, daga yaro har babba, kuma ko mazaunin ina ne. Amfanin gyada na da yawa ga mai bukatarta. Ana iya cin gyada […]
A wannan makon zan fara bayanin yadda dan kasuwa zai sarrafa gyada domin sayarwa a kasuwanninmu na gida da na waje. Ita dai gyada ba ta bukatar gabatarwa ga duk wani mazaunin kasar nan, daga yaro har babba, kuma ko mazaunin ina ne. Amfanin gyada na da yawa ga mai bukatarta. Ana iya cin gyada danya, ko a gasa ta, ko a dafa ta, ko ma a soya ta a ci. Ana yin miya da gyada, hakazalika ana yin miya da man gyada, a kuma yi kayayyakin marmari iri-iri a ciki har da alawar gyada . Ana iya matse gyada a samu kuli-kuli, ko tunkuza a kuma samu man gyada. Kamfanoni na amfani da gyada wajen yin kayayyakin abinci irin su biskit da abincin dabbobi da makamantansu, bayan sun tatse man da ke cikinta.
Matan karkara na sarrafa gyada wajen yin kuli-kuli da man gyada, inda suke amfani da injin nika da turmin daka da sauran mazubai wajen tatse man gyada, daga jikin markadaddiyar gyada. Akwai masana’antu manya da kanana na yin man gyada a garuruwa da biranen Arewacin kasar nan.
A kimiyyance, masana sun tabbatar da kasancewar sinadarai da jikin mutum ke bukata a cikin gyada, irin su Bitamin (bitamin) ajin ‘E’, da ‘Nacin’ da ‘Calcium’ da ‘Phosphorous’ da ‘Zinc’ da sauransu. Haka kuma Hukumar Abinci ta Duniya (FAO) ta hakikance cewa gyada ita ce nau’in abinci ta 13 a sikelin muhimmancin kayayyakin abincin duniya. Kuma gyada ce ta hudu cikin nau’ikan abinci mafi muhimmanci a kwayoyin abinci da ake samun man girki. Wannan inganci na gyada a matsayin kayan abinci ya sa al’ummar duniya suke bukatarta sosai. Haka kuma ya sa kusan babu inda ba a amfani da ita a cikin duniya.
Wannan muhimmanci ya sa gyada ta zama wata aba da manoma a duniya suke nomawa a matsayin abin da za su noma su sayar su samu kudin shiga, domin biyan bukatunsu na yau da kullum, ba wai a matsayin abinci ba. A Arewacin Najeriya inda ya kasance a taswirar noma da sayar da gyada a duniya, saboda yawan shekarun da aka yi ana fitar da gyada ya zuwa kasuwannin duniya, musamman ma kasar Birtaniya, inganta yawaitar ta na da nasaba da wannan bukata.
Masana tarihin tattalin arzikin kasa sun ce Turawan mulkin mallaka ne suka kawo gyada Afirka, musamman ma nan Najeriya, domin bukatar da kasarsu ke da ita ta wadata da man gyada, domin abinci da kuma tunkuzar gyada, domin yin kayan marmari da abincin dabbobi. A daidai lokacin da su ka kawo gyada ne, kuma su ka sa haraji domin tara kudaden da za a samar wa al’umma kayayyakin more rayuwa da tafiyar da harkar mulki da tsaro a tsakanin al’umma, sannan a lokacin ne kuma suka gabatar da kudin zamani, inda suka ankarar da jama’a ga noman gyada da sauran albarkatun gona irinsu auduga da koko da za su saya su kai kasarsu, su kuma manoman su samu kudin biyan haraji daga yin hakan.
In Allah Ya kai mu makon gobe zan yi bayanin yadda dan kasuwa zai sayi gyada ya sarrafa ta, domin sayarwa a kasuwannin gida Najeriya da na kasashen ketare.