Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (10)

A makon da ya gabata na yi alkawarin tattauna sauran hanyoyin da dan kasuwa zai bunkasa kasuwar kuli-kulinsa a kasuwannin gida da na kasashen ketare, wato kari a kan wadanda na yi a makon jiya. A kuma wannan makon ne nake da niyyar duba yadda ake sarrafa gyada a zamanance, a karami da babban matsayi, […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (10)
Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (10)

A makon da ya gabata na yi alkawarin tattauna sauran hanyoyin da dan kasuwa zai bunkasa kasuwar kuli-kulinsa a kasuwannin gida da na kasashen ketare, wato kari a kan wadanda na yi a makon jiya. A kuma wannan makon ne nake da niyyar duba yadda ake sarrafa gyada a zamanance, a karami da babban matsayi, domin fitar da manta da kuli-kuli, domin amfanin al’umma.
Idan ana biye da ni, za a iya tunawa na tattauna girman kasuwar kuli-kuli a kasar nan da ma yadda dan kasuwa zai iya fadada ta a cikin kasar nan, inda na ba dan kasuwa shawarar kai hajarsa manyan shagunan kasar nan. Na kuma ba shi shawarar yadda zai inganta ta, ta bangaren mazubi da yi ma ta rijista da Hukumar NAFDAC. To idan dan kasuwa zai iya yin haka, ya kuma cika ka’idojin Hukumar NAFDAC, dan kasuwa zai iya fitar da kuli-kulinsa ya zuwa kasashen ketare.
Abin da dan kasuwa zai yi na farko domin fitar da shi ya zuwa kasashen ketare, shi ne na ya nemi kasuwar hajarsa. Idan mai karatu na biye da ni, zai iya tunawa na yi makalu da yawa a kan nema wa haja kasuwa a ciki da wajen kasar nan. Duk da haka, wannan ba zai hana na yi wa mai karatu matashiya ba. Neman kasuwa domin sayar da haja a kasashen waje na farawa da tantance kasashen da yake son ya sayar da hajarsa. Idan ya yi haka zai kasance yana da zabin hanyar da zai tallata hajar tasa, walau ta kafar intanet ko cibiyoyin kawancen kasuwancin kasar ko kasashen (Chamber of Commerce) da yake so ya sayar da hajar tasa ko kuma ta ofisoshin jakadancin wadannan kasashen. dan kasuwa na kuma iya tallata hajar tasa ta kungiyoyin kasuwanci masu fitar da kaya ya zuwa kasashen waje. Misali, kungiyar ’yan kasuwa masu fitar da koko ko karo ko masu fitar da auduga da dai sauransu. Akwai kuma kafofi ta shiyyar Hukumar Habaka Fitar Da Kayayyaki Zuwa kasashen ketare (Edport Promotion Council).
Har ila yau dai, ba sai na yi wa mai karatun shafin nan ba bayani a kan yadda zai fitar da kuli-kuli ya zuwa kasuwannin ketare ba, in ya samu masu saye. Na yi Makalu da yawa a kan fitar da kayayyaki daban-daban, musamman ma dangin abinci irin su rogo da doya da yazawa da waken soya da dai sauransu. Bambancin fitar da kuli-kuli ita ce, shi kuli-kuli wani abu ne da za a iya ci kai tsaye ba tare da bukatar wata sarrafawa ba. Saboda haka ina shawartar dan kasuwa da ya kara neman shawara ga hukumomin binciken abinci domin inganta dadewar kuli-kulin a cikin mazubinsa.    
Idan muka koma wajen sarrafa gyada domin yin kuli-kuli a zamanance, za a ga cewa hanyoyin ba su bambanta da wanda na yi bayani ba a lokacin da nake bayanin hanyar gargajiya ta sarrafa gyada, domin yin kuli-kuli da mansa. Bambancin a nan shi ne, duk ayyukan da injina ne. Ana wannan harkar a babban matsayi a kasar nan tun lokacin mulkin Turawa, saboda haka akwai wadannan injina a manyan biranen kasar nan da ke shiyyar Arewa da ake samun gyada, musamman ma birnin Kano. A rin wadannan masana’antu manya na bukatar babban jari domin samun saye da kebe babban wuri ko hayar babban wuri da za a saya a kuma zuba manyan injina. Ana iya yin matsakaiciya da karamar harkar kuli-kuli a zamanance, wato a masana’antu irin wannan.    
Mai karatu kuma zai lura cewa kuli-kulin da ake fitarwa a masana’antu, wato ta hanyar zamani, tunkuza ce da ake abincin dabbobi da sarrafawa domin yin sauran kayayyakin masana’antu.