Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (11)

Zan yi bayani akan yadda dan kasuwa zai sarrafa gyada ta hanyar zamani domin sayarwa da kamfanoni da sauran jama’a masu amfani da kayayyakin da aka fitar daga cikinta a cikin kasa da wajen Najeriya. A makon da ya gabata na fara bayani akan sarrafa gyada, domin yin kuli-kuli ta hanyar zamani, inda na yi […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (11)

Zan yi bayani akan yadda dan kasuwa zai sarrafa gyada ta hanyar zamani domin sayarwa da kamfanoni da sauran jama’a masu amfani da kayayyakin da aka fitar daga cikinta a cikin kasa da wajen Najeriya. A makon da ya gabata na fara bayani akan sarrafa gyada, domin yin kuli-kuli ta hanyar zamani, inda na yi bayanin cewa ita wannan hanya ba ta bambanta da ta gargajiya ba wacce na yi bayanin ta a makonnin baya ba. Babban bambancin guda daya ne, wato kusan komai da injina ake yi, maimakon yadda ake mafi yawancin al’ammuran da hannu a hanyar ta gargajiya.
A mukalar makon jiya, harkar sarrafa gyada a zamanance masanantu ba bakuwa ba ce a kasar Hausa, inda na cewa mai karatu zai iya samun irin wadannan masana’antu a manyan garuruwan Arewacin Najeriya, musamman ma Birnin Kano. To sai dai mafi yawancin irin wadannan masana’antu da ke sarrafa gyada manya ne. Amma daga bisani, bayan  an sami tsaiko a yawan gyadar da ake samu a Najeriya, da harkar sarrafa gyada ta ja baya sakamakon haka, sai kanana da matsakaitan masana‘antu suka rika tasowa. Kuma wadannan masana’antu na amfani da kananan injina masu saukin kudi da saukin sarrafawa fiye da wadanda aka rika amfani da su a baya, wadanda kuma ake yi a kasar nan.
Shi kuli-kulin da ake yi a irin wadannan masana’antu ya bambanta da na gargajiya, domin shi ba a kara masa gishiri ko sukari, domin ba domin a ci ake yin sa ba. Kuma irin wannan kuli-kuli na masana’antu manya-manya ake yin sa, sabbanin na gargajiya da ake yin sa kanana. Sannan kuma ba a soya wannan kuli-kuli kamar kuli-kulin gargajiya, inji na fitar da shi da zarar ya tace man da ke jikin gyadar, wannan ya sa wasu ke kiransa tunkuza. Shi kansa man gyada da ake samu daga kafar zamani ta masana’antu ya bambanta da man kuli-kuli na gargajiya, domin ba shi da kamshi kamar yadda man kuli-kuli na gargajiya yake. Hakan ya kasance saboda ana soya man kuli-kulin gargajiya yayin da ake kuli-kuli, ana kuma soya gyadar da aka yi tunkuzar da aka samu man kafin a nika ta a inji. Shi kuwa man kuli-kulin da aka fitar daga masana’antu ba a soya gyadar da za a fitar da shi, ko kuma a soya shi yayin da ake kuli-kulinsa. Ana kiran wannan maid a lakabin kwantarola, kuma farashinsa bai kai na man kuli-kulin gargajiya ba.
Masana’antu na sayen kuli-kulin da aka yi a zamanance domin yin wasu kayayyakin masarufi kamar su biskit da abincin dabbobi da dai sauransu. Manoma masu kiwon shanu na sayen irin wannan kuli-kuli domin bai wa dabbobinsu a matsayin abincin da zai ba dabbobinsu kuzari su kuma yi girma da maiko.  Irin wannan kuli-kuli na masana’antu na da farin jini a masana’antun gida da na kasashen waje. Ana zuba kuli-kulin a cikin buhunan garara masu nauyin kilo 50, wanda kuma saboda wannan tsayayyen mizanin, kuli-kulin ke da tsayayyan farashi a kasuwannin cikin gida da na kasashen ketare, duk da cewa wannan farashi na bambanta daga lokaci zuwa lokaci.
Ana zuba wannan kuli-kuli a buhunan garara domin ya samu iska kada ya lalace. Wannan kuma na bai wa kuli-kulin tsawon kimanin shekaru biyar bai lalace ba. Farashin kuli-kulin kuma na kasancewa daidai da dadewarsa, wato sabon kuli-kuli na fin tsohon kuli-kuli farashi a kullu-yaumin. A wannan dalilin ne ma masu sayen kuli-kuli daga kasashen ketare ke bayar da adadin iya lokacin da kuli-kulin da suke bukata, misali, su ce kuli-kulin da suke so kada ya wuce wata 18 da yi.
Kuma ana bin tsarin zaben gyada irin na kuli-kulin gargajiya, kamar yadda na yi bayani a baya, yayin da ake zaben gyada domin yin kuli-kulin zamani.