Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (12)
A makalar wannan makon zan yi bayanin yadda dan kasuwa zai sarrafa gyada domin sayar da ita a kasuwannin kasashen waje a matsayinta na gyada ba wani abu da aka yi, ko ake samu daga gareta ba. Ana fitar da gyada a daga Najeriya wannan siffar ya zuwa kasashen waje tun zuwan Turawan mulkin mallaka. […]
A makalar wannan makon zan yi bayanin yadda dan kasuwa zai sarrafa gyada domin sayar da ita a kasuwannin kasashen waje a matsayinta na gyada ba wani abu da aka yi, ko ake samu daga gareta ba. Ana fitar da gyada a daga Najeriya wannan siffar ya zuwa kasashen waje tun zuwan Turawan mulkin mallaka. Kuma a yadda noman gyada ya inganta a wani lokaci baya, Najeriya ke wadata kasuwannin duniya da kimanin kashi 40 daga cikin 100 na gyadar da ake sayarwa a kasuwannin duniya.
Kusan duk dan Najeriya mai kimanin shekara 50 a duniya da ya girma a Arewacin kasar zai bayar da labarin ganin fulotan awon gyada a garuruwan Arewacin Najeriya, inda ’yan kasuwa ke sayen gyada daga hannun manoma. Wadannan yan kasuwa na zuba gyadar da su ka saya a buhuna, sai su tara ta a wadannan fultai motoci su dauka su kai garuruwa da biranen da ke da tashoshin jirgin kasa irin su Kano da Guru da Malam Madori da Kauran Namoda da Zariya da dai sauran su. Jirgin kasa zai dauke wannan gyada ya kai ta Legas inda za a zuba ta a jirgin ruwa akai ta kasashen ketare, musamman ma ingila.
A birnin Kano kuwa, saboda yawan gyadar da ake tarawa kafin jirgin kasan ya zo ya kwashe ta zuwa Legas, har ma dalarta ake yi a rufe da tamfol. Ita dalar gyada, ga wanda bai sani ba, buhunan gyadar ake jerawa su yi fadi fiye da girman matakaicin gida, sai a rika dorawa fadin ana rage fadin yayin da tudun na karuwa har sai ya yi tsayin da akarshe buhu daya ne zai iya zama. Tsayin dala na fin tsayin duk wani gidan bene da mutum ka iya tunanin tsayinsa a Arewacin Najeriya. Saboda mahimmancin gyada a tarihin tattalin arzikin Najeriya, an rika saka hoton dalar gyada a kudin kasar.
Dalar gyada a Birnin Kano da ma fulotan gyada a garuruwa da biranen kasar nan sun fara bacewa yayin da hakar man fetur ya fara inganta a kasar nan, daidai da karyowar shekarar 1970, inda man fetur ya maye gurbin gyada da sauran albarkatun gona da kasar ke sayarwa sauran kasashe, domin samun kudin shiga, irin su auduga da koko da kwakwar manja da makamantansu. Tsabar gyada da kulikulin tunkuza da man gyada sun kasance fiye da kasha 70 daga cikin 100 na kudin shiga da Najeriya ta samu daga kasashen waje daga shekarar 1956 ya zuwa 1967.
Yawan gyadar da Najeriya ke fitarwa ya zuwa kasuwannin duniya ta ragu daga kimanin tan dubu 502 a shekarar 1961ya zuwa tan dubu 291 a shekarar 1970. Haka yawan gyadar da ake fitarwa ya rika raguwa daga shekara zuwa shekara, har ya kasance Najeriya ba ta iya fitar da ko buhu daya a daidai shekarar 1980. Masana sun ce ba mai da hankali akan hakar man fetur kadai ya rage yawan gyadar da ake fitarwa ba, al’amarin ya hada da billar wata cutar da ta rika kama gyadar saboda nomata a wuri daya kowace shekara, da kuma fari da ya rika afkuwa a Arewacin Najeriya a cikin wadannan shekarun.
A yau Najeriya na noma kimanin tan miliyan biyu na gyada, wanda ya kai kimanin kasha biyar daga cikin 100 na gyadar da ake nomawa a duniya. Amma kalilan ne daga cikin wannan adadi Najeriya ke fitarwa ya zuwa kasuwannin duniya, ana cinye mafi yawanta a cikin kasar kama daga soyayyiyar gyda ya zuwa dafaffiya, har ya zuwa kulikulin ci da tunkuzar dabbobi da man da ake samu daga gyadar ta fiton gargajiya da na masana’antu kamar yadda na yi bayani a makalun baya. Zan tashi daga nan idan Allah Ya kaimu makon gobe.