Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (13)

Wannan ita ce makala ta karshe a kan bayanan da nake yi a kan yadda dan kasuwa zai sarrafa gyada domin sayar da ita a kasuwannin gida da na kasashen waje. A wannan makon zan dora a kan inda na tsaya a makon jiya, wato yadda dan kasuwa zai sarrafa gyada ya fitar da ita […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (13)
Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (13)

Wannan ita ce makala ta karshe a kan bayanan da nake yi a kan yadda dan kasuwa zai sarrafa gyada domin sayar da ita a kasuwannin gida da na kasashen waje.

A wannan makon zan dora a kan inda na tsaya a makon jiya, wato yadda dan kasuwa zai sarrafa gyada ya fitar da ita ya zuwa kasuwannin ketare a matsayinta na gyada ba wani abu da aka yi, ko ake samu daga gare ta ba.
A shimfidar da na yi a makalar makon jiya, na yi bayanin cewa wannan tsohuwar harka ce, inda na yi bayanin yadda ake fitar da gyada daga Najeriya a wannan siffar zuwa kasashen waje tun lokacin Turawan mulkin mallaka. Kuma a yadda noman gyada ya inganta a wani lokaci baya, har Najeriya take wadata kasuwannin duniya da kimanin kashi 40 daga cikin 100 na gyadar da ake sayarwa a kasuwannin duniya.
    To, matakin farko da zai kai dan kasuwa ga nasara a wannan harkar shi ne, zaben gyadar da zai sarrafa domin fitar da ita zuwa kasuwannin duniya. Idan mai karatu na biye da ni a wannan fili, idan ya waiwaya zai iya tuna cewa na yi makala a kan irin garuruwa da wuraren da zai sayi gyada, da ma irin lokacin da ya kamata ya shiga irin wadannan kasuwanni, domin samun sirrin farashin gyada a kasuwanni da kuma samun sukunin zaben irin gyadar da ta dace a kasuwannin.
Na kuma ba dan kasuwa hasken yadda zai sarrafa ya kuma ajiye gyadar da ya saya, walau domin amfani da ita wajen tatsar man ta da fitar da kuli-kuli ko tunkuza, ko kuma domin sayar da ita a haka zahirinta a kasuwanninmu na gida da na kasashen waje.  
    Saboda haka ina shawartar dan kasuwa mai niyyar fitar da gyada zuwa kasuwannin ketare da ya bibiyi wadannan makaloli na baya, domin samun karin bayanin da zai taimaka masa kwarai da gaske wajen saya da sarrafawa da ajiye gyada,  domin safararta zuwa kasuwannin duniya.
Wani abu mai mahimmanci da zan ja hankalin dan kasuwa wajen saye da sarrafa gyada domin fitar da ita zuwa kasashen waje shi ne lafiyarta. Domin babbar matsala da zai fuskatanta a wannan harkar tun daga gida Najeriya ita ce, samun gyada mai lahani a cikin gyadar da zai fitar da ita zuwa kasashen ketare.  
A makalolin baya da na yi a kan yadda dan kasuwa zai fitar da albarkatun gona zuwa kasashen ketare, na yi bayanin irin binciken da ma’aikatan Hukumar Killace Albarkatun Gona da Dabbobi (Plant and Animal kuarantine) ke yi a kan iyakokinmu da tasoshin jiragen sama da na ruwa.
Doka ta ba hukuma damar hana fitar da dabba da kowane albarkutun gona da ke da lahani zuwa kasashen waje. Saboda haka wannan na iya sa hukumar ta hana dan kasuwan da bai tsabtace gyadarsa shi fitar da ita, sannan ko da ya iya fitar da gyada mai lahani, to zai sake iske irin wannan hukumar a kasar da zai kai gyadar, wacce kuma za ta iya fin ta Najeriya sa ido da tsaurarawa wajen tantance lafiyar gyadar; saboda haka za su iya dawo da ita Najeriya a cikin gaggawa, su sa dan kasuwa yin asara.  
Kasuwar gyada a kasashen duniya ta fi ta kowane albarkatun gona da mu ke da shi a Najeriya. Wannan ya sa ba sai dan kasuwa ya samu oda daga abokan ciniki na kasashen waje ba, kafin ya fara tanadar gyadar da zai sayar musu ba, kamar sauran albarkatun gona. Kuma kasuwar gyada kodayaushe a bude take daga farkon shekara har karshenta, ba kamar sauran albarkatun gona ba da suke da lokutan da kasuwarsu ke ci a wadannan kasashe ba. Albishir din da zan yi wa dan kasuwa a kan wannan harka shi ne, ribarta na ribanya uwar kudi, wani lokacin fiye da sau biyu, idan dan kasuwa ya bi ka’ida ya kuma kai irin gyadar da ake so a irin wadannan kasuwannin. Kuma akwai yunkurin ingantawa da farfado noman gyada a Arewacin Najeriya, daga gwamnati da wasu hukumomin binciken aikin gona na duniya.