Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (2)

Masu karatu sun ja hankalina a kan wani abu da suke gani tamkar tsambare na yi musu a mukalar makon jiya da na yi a kan gyada a wannan filin. Suka ce, a bisa al’ada nakan yi bayani da tarihi na kowane daya daga cikin albarkatun gona da na dauka na yi mukalar sarrafa shi […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (2)
Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (2)

Masu karatu sun ja hankalina a kan wani abu da suke gani tamkar tsambare na yi musu a mukalar makon jiya da na yi a kan gyada a wannan filin. Suka ce, a bisa al’ada nakan yi bayani da tarihi na kowane daya daga cikin albarkatun gona da na dauka na yi mukalar sarrafa shi domin kasuwanninmu na gida da kasashen ketare.
A makon da ya gabata da na gabatar da gyada, suka ce ban yi hakan ba, suka kuma ce a bisa al’ada ban yi bayani a kan kasashen da ake samun ta ba da kuma kasashen da ake bukatarta a duniya. Suka ce kuma raunin mukalar ba nan kadai ya tsaya ba, bayanin da na yi a kan amfanin gyada a mukalar baya ya tsaya ne a kan amfanin ta tsakanin iyali, daga inda aka dauko ta daga gona zuwa sarrafa ta a gida, wato ba a masana’antu ba.
Zan duba wadannan abubuwa da aka la’akarantar da ni da kuma wasu abubuwan da ka iya samu a makalar wannan makon. Masana tarihin tattalin arzikin kasa na duniya  sun hakikance cewa ita gyada dai an fara shuka ta a lardin Kudancin kasar Bolibia da lardin Arewa maso Yammacin kasar Ajentina, kafin shigar Turawan mulkin mallaka ’yan asalin kasar Sifen (Spain) cikin wadannan kasashe;  dukkan wadannan kasashen na cikin Nahiyar Kudancin Amurka ne.
Masana tarihi na kyautata zaton cewa, ’yan kasuwar kasar Sifen ne suka baza gyada ya zuwa nahiyoyin Asiya da na Afirka. Idan mai karatu bai manta ba na yi bayani a makalar baya cewa Turawan mulkin mallaka ne suka kawo gyada Afirka: To idan aka lura, Turawa sun shigo Afirka da farko a matsayin ’yan leken asirin kasa, inda suka fake da cewa matafiyan bude ido ne da gano taswirar duniya, irinsu Mungo Park; sai kuma suka dawo a matsayin ’yan kasuwa, irin su Richard Lander; sannan kuma suka dawo a matsayin masu yada addani, wanda daga bisani suka dawo a matsayin ’yan mulkin mallaka.
A yanzu haka ana noma gyada a kimanin kasashe fiye da dari a duniya, inda mafi yawancin ta ake nomawa a kasashen Indiya da Sin (China) da Amurka da Najeriya da Myanmar. Miliyoyin kananan manoma na noma gyada a kasashen Afirka da ke kudu da Hamadar Sahara, domin abinci da samun kudin bukatun yau da kullum. Wadannan kasashen Afirka sun hada da Senegal da Najeriya da Gambiya da Mali da Burkina Faso da kuma Nijar.
Najeria da Senegal su ne suka fi noman gyada a Afirka, inda suke samar da fiye da kashi 45 cikin 100 na gyadar da ake noma wa a Nahiyar Afirka. Sannan kuma ita kanta Najeriya ke samar da kimanin kashi biyar cikin 100 na gyadar da ake nomawa a duniya, inda take noma fiye da tan miliyan biyu daga cikin tan miliyan 25 da ake nomawa a duniya, bisa kiyasin shekarar 2010.
    Wannan yawan gyada da Najeriya ke nomawa bai kai rabin abin da kasar ke nomawa a kimanin shekara 40 da su ka shude ba. A tsakanin shekarun 1956 ya zuwa 1967, gyada da manta sun kasance fiye da kashi 70 na albarkatun kasa da Najeriya ke fitarwa zuwa kasuwannin duniya. Duk mai shekara 50 da dori ba zai kasa sanin dalar gyadar Kano ba, haka kuma daliban tarihi da na yanayin kasa na da labarin tasirin da gyada ta yi a tayar da tattalin arzikin kasar nan. Zuwan man fetur da kuma wasu cututtuka da suka tasowa gyada da kuma rashin bincike da inganta tsuranni suka kawo tabarbarewar noman gyada a kasar nan.   
    Zan tashi daga nan idan Allah Ya kai mu makon gobe, inda zan fara da wuri da yadda dan kasuwa zai samu gyada a Najeria da yadda zai sarrafa ta domin sayarwa ga al’ummar kusa da shi da kuma masana’antun gida Najeriya da kuma masu masu bukatar gyadar da albarkatunta a kasuwannin duniya.