Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (5)

A makon jiya ne na yi shimfidar yadda farashin gyada ke kasancewa daga lokaci zuwa lokaci a cikin shekara. Wannan zai ba dan kasuwa hasken yadda farashi yake a kowane lokaci ya yi shawarar sayen gyada, sannan na ba dan kasuwa shawarar wurare da irin kasuwannin da zai je domin sayen gyadar da zai sarrafa, […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (5)
Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (5)

A makon jiya ne na yi shimfidar yadda farashin gyada ke kasancewa daga lokaci zuwa lokaci a cikin shekara. Wannan zai ba dan kasuwa hasken yadda farashi yake a kowane lokaci ya yi shawarar sayen gyada, sannan na ba dan kasuwa shawarar wurare da irin kasuwannin da zai je domin sayen gyadar da zai sarrafa, wato inda zai same ta da sauki da kuma yawa, ya kuma zabi irin wacce yake so.     
   Na ba dan kasuwa shawarwari da yawa game da yadda zai sayi gyada a irin wadannan kasuwanni, inda a karshe na ce zan yi bayani a kanta, ita ta ya je kasuwar da zai sayi gyada da wuri, misali da hantsi, domin nazartar yadda kasuwar za ta kasance, yadda zai sayi gyadar da sauki ya kuma samu wacce yake so.
Na yi bayanin ire-iren gyada da ake da ita da kuma bukatun masu amfani da su. Wasu masu amfani da gyada, kuma masu mahimmancin gaske da ban yi bayanin su a kasidun baya ba, su ne masu cin ta hakanan zalla ko tare da wani abinci kamar garin kwaki ko burodi ko wasu sauran nau’in abinci. Masana sun ce kashi daya bisa uku na gyada masu cin ta haka zahiri ke taune ta.
    To rashin isasshen fili ba zai bar ni in ci gaba da karin bayani a kan dabarar sayen gyada ba. Sai dai wannan ba zai hana in ba dan kasuwa shawara wajen zabar gyadar da zai saya ba, wajen kiyasta darajarta.
Babban abin lura a sayen gyada kowacce iri ce shi ne, kyanta. Kada dan kasuwa ya manta ina maganar gyada bararriya ba mai kwanso ba. To gyada mafi kyau ita ce, wacce ba ta da ‘bori’a cikinta. Ita bori damejin gyada ce da kwari su ka bata.
dan kasuwa zai gan ta ba ta da jar fatar da aka san gyada da ita, walau ta yi baki ko ta yi ruwan kasa. Ko da yake da wuya dan kasuwa ya ga gyada babu bori a cikinta, amma yawan bori a cikin gyadar da dan kasuwa ya cika hannunsa domin ya duba na zama mizanin awon kyan gyadar.
    Ya zama al’ada ga masu sayen gyada ko wani hatsi a kasuwa da su debe shi a tafin hannunsu daidai gwargwadon iko su duba. Yayin da dan kasuwa ya debi gyada ya ga yawan bori a hannunsa ya wuce kwaya biyu daga cikin sauran kwayoyin gyadar da sun kai kimanin 20 a cikin samfarin da ya debo, to wannan gyadar ba ta da kyawu, kada ya saya.
dan kasuwa zai dumtsi gyadar ne ya duba idan an zuba ta a manyan mazuban awo domin sayarwa, in kuwa a cikin buhuna take, zai yi amfani da wani karfe ragadadde mai kama da kahon saniya da ake cewa ‘kahon cukuman’ ya soki buhun gyadar a tsakiyarsa da wannan karfen, inda gyadar za ta biyo ragadar kahon ta fito. dan kasuwa zai tara hannunsa a karshen kahon ya rike samfurin gyadar ya duba. Yawan bori a cikin wannan samfur din zai ba dan kasuwa gane gaskiyar kyawun gyadar.
    Wani sirri kuma na sayen gyada mai kyawu a kasuwa shi ne, kasancewar rabin gyadar bai kasance ba a kwankatse take ba, wato mafi yawancin kwayoyinta ba su fashe ba. Sai sirrin sayen gyada na uku, dan kasuwa ya tabbatar ya sayi sabuwar gyada, wato wacce ba ta shekara ba, domin ta fi maiko, ta kuma fi nagarta a game duk abin da zai yi da ita; domin gyada tana dada tsufa darajar na dada ragu. Zan tashi daga nan idan Allah Ya kai mu makon gobe.