Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (6)
Sarrafa gyada na iya kasancewa launi biyu, walau dan kasuwa ya sarrafa gyada domin sayarwa a kasuwannin gida, ko ya sarrafa ta domin fitar wa kasuwannin qasashen qetare. Kamar yadda nayi bayani a baya, na ce nasarar sarrafa gyada a samu riba ya danganta da yanayin da dan kasuwa ya saye ta, wato kyawunta da […]

Sarrafa gyada na iya kasancewa launi biyu, walau dan kasuwa ya sarrafa gyada domin sayarwa a kasuwannin gida, ko ya sarrafa ta domin fitar wa kasuwannin qasashen qetare. Kamar yadda nayi bayani a baya, na ce nasarar sarrafa gyada a samu riba ya danganta da yanayin da dan kasuwa ya saye ta, wato kyawunta da sauqinta. Domin komai kyawun gyada, idan ba a same ta a kan farashi mai sauqi ba, to ba za a samu riba mai kauri ba. Sannan kuma komai arahar gyada idan ba a same ta da kyau ba, to ba za a ci gajiyarta ba. Wannan ya sa na dauki lokaci ina bayanin yadda dan kasuwa zai samu nasara a sayen gyada, inda zai same ta da kyawu da sauqin kudi.
Sarrafa gyada domin kasuwanninmu na gida, na kasancewa sarrafa gyada domin buqatar masu saye su ci. Yanzu martabar gyadar ce ta tashi daga kan faifai ko tiren da tsofaffi ke sa wa gaba a cikin unguwa ko dauke a kan yara ’yan mata, ya zuwa wurare na alfarma a cikin manyan kantuna a garuruwa da manyan biranen qasar nan. Ana samun gyada a mazubai iri-iri, kama daga leda ya zuwa manyan kwalabe. Likkafar gyada ta ci gaba da yanzu za ka ajiye gyada a kan teburin da manya ke taro, suna ci ana tattauna al’amura. Haka kuma ana tarar baqi da kwalbar gyada a gidajen ’yan boko. Wannan na nuna yadda kasuwar gyadar da aka sarrafa domin ci ke habaka a qasar nan.
dan kasuwa zai lura da cewa gyadar da ake sarrafawa a sayar a wadannan kantuna na alfarma domin ci, ta bambanta da gyadar gargajiya da muka sani mai qananan qwayoyi, domin ita wannan ta dan dara waccar a girman qwayoyi. Ana dafa gyadar da za a ci a saka mata gishiri, amma ba a bari ta dahu da yawa. Za a debe ta daga cikin ruwa a tsane ta a shanya ta sha iska. A gargajiyance za a yayyafa mata farar qasa a birshine ta yayin da ta fara bushewa, domin kada ta qone yayin suyar ta. Sai a soya ta a cikin kaskon da aka zuba farin rairayi daidai qima. Za a ci gaba da juya ta cikin wannan kasko da cokalin suya ko wani majuyi a-kai-a-kai don kada ta qone.
Kusan hanyar zamani ta soya gyadar ci daya da ta gargajiya da na yi bayani a sama, sai dai akwai abin suyar da za a iya amfani da shi a zamanin yanzu, musammanma wajen soya gyada mai yawa, domin babbar kasuwa, da ake kira da Turanci ‘Fryer’, wanda dan kasuwa zai yi amfani da shi. A wannan tsarin na zamani, dan kasuwa ba zai yi amfani da farar qasa ko rairayi ba. Kuma maimakon ya kai gyadar ci kasuwa da bawonta, inda mai ci sai ya murmushe ta ya hure bawon a tsarin gyadar gargajiya, ita wannan gyada ta zamani sai dan kasuwa ya murje ta fatar ta fita an tsabtace ta kafin a zuba ta cikin mazuban da za a kai ta kasuwa.
dan kasuwa zai lura cewa kashi 90% cikin 100 na qwayoyin wannan gyada bai fashe ba yayin dafa ta ko murje ta da bushe ta daga cikin fatarta ba, domin tsabtace ta don a kai ta kasuwa. Ya zama dole dan kasuwa mai niyyar sarrafa gyada domin ci ya yi la’akari da irin wannan gyada a kasuwa in ya je saye. Ba wuyar samu gare ta ba, sabon iri ne da ma’aikar gonar ta samar a shekarun baya, wanda ke iya yi har a wasu shiyyoyin da a wasu shekaru ba a san su da yin gyada ba, kamar jihohin gabashin qasar nan.
Zan duba kafofin sarrafa gyada, irin su quli-quli da tunkuza da dai sauransu, domin sayarwa a kasuwanninmu na gida Najeriya da qasashen qetare idan Allah Ya kai mu makon gobe.