Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (7)

A wannan makon ne zan duba kafofin sarrafa gyada, irin su kuli-kuli da tunkuza da dai sauransu,  domin sayarwa a kasuwanninmu na gida Najeriya da kasashen ketare, kamar yadda na yi alkawari a makon jiya. Idan mai karatu na biye da ni zai tuna cewa a makon jiya na yi mukala a kan yadda dan […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (7)
Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (7)

A wannan makon ne zan duba kafofin sarrafa gyada, irin su kuli-kuli da tunkuza da dai sauransu,  domin sayarwa a kasuwanninmu na gida Najeriya da kasashen ketare, kamar yadda na yi alkawari a makon jiya. Idan mai karatu na biye da ni zai tuna cewa a makon jiya na yi mukala a kan yadda dan kasuwa zai sarrafa gyada domin ci, ya sayar a kasuwannin gida.
Sarrafa gyada domin samun manta da kuli-kuli na iya kasancewa kashi biyu, watau hanyar gargajiya da ta zamani. Kuma bambancin hanyoyin biyu shi ne amfani da injina kusan gaba daya a hanyar ta zamani. Ita kuwa ta gargajiya na amfani da hannu wajen yin mafi yawancin ayyuwan kuli-kuli, inda a karo daya ne kawai aikin zai shiga inji kamar yadda za mu gani. Amma duk da haka tsari daya ne ake bi wajen tatse mai daga jikin gyada a samu kuli-kuli ko tunkuza, walau ta tsarin gargajiya ko ta fannin zamani na amfani da injina.
Za a fara soya gyada sama-sama, wato ba ta soyu kwarai ba, amma a soya ta daidai gwargwadon iko ba tare da an bari ta kone ba. Yin haka zai fito da manta, sai a sauke ta ta huce, kafin a kai ta injin nika a markada ta. Ana markada gyada a injin nikan da ake amfani da shi wajen nikan sauran hatsin abinci irin su gero da dawa da masara da alkama da dai makamantansu. Sai dai markaden gyada ba kamar na wake ba ne ko na kayan miya, inda za a rika zuba ruwa yayin da ake markadawa. Markaden gyada ba sa masa ruwa ko kadan.
Markadaddiyar gyada na kasancewa da kauri kititif. Wanda zai sarrafa ta zai zuba ta a turmin daka mai fadi, da zaran ta yi sanyi domin za ta kasance da dumi yayin da ta baro cikin injin nika. A nan ne za a yi wa gyada abin da ake ce wa ‘Fito,’ Za a zuba markadaddiyar gyadar kimanin rabin abin da turmin zai iya ci saboda mai zai rika taruwa a cikin turmin ana kwashewa yayin da ake fiton gyadar. Shi fito ana yin shi ne da tabarya, inda za a saka tabaryar cikin markadaddiyar gyadar da aka zuba a turmin fiton, a rika juya tabaryar a ciki, inda gyadar za ta ci gaba da yin kauri, mai yana fita ana kwashewa ana tarewa waje daya, har sai an ga man ya fara kafewa.
Yayin da aka ga man ya ragu ainun, sai a kwashe wannan gyadar da aka yi wa fito, wato aka fitar da man ta, sannan ta hade ta yi tauri, ta zama tunkuza. Za a zuba tunkuzar a babban mazubi, ana daukar ta da kadan-kadan ana dorawa a kan dutsen nika, inda za a daga bayan dutsen inda mai nika za ta durkusa, a karkatar da karshen dutsen da zai kasance an saka wani mazubi da zai rika taryar man da zai gangaro daga gare shi yayin da ake murzar wannan tunkuzar. Ita murza ana yin ta ne da hannu, inda za a rika murtsuka tunkuzar akan dutsen nikan ana fitar da sauran man da ya rage, har sai an ga an tatse mafi yawancin man da rage.
Za a tara wannan tunkuzar da aka murje aka fitar da man wuri daya. Shi ma man da aka samu daga murza za a hada shi da wanda aka samu daga fito. Za a zuba wannan mai a kaskon nika, wanda a yanzu kwano ne na karfe, a dora a wuta a sa man ya yi zafi. Za a rika gutsuro wannan tunkuza kanana, daidai bukata, ana sakawa a cikin wannan mai ana soyawa domin yin kuli-kuli.
Zan tashi daga nan in Allah Ya kai mu makon gobe.