Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (8)

A makon da ya gabata na yi makala a kan yadda za a sarrafa gyada, domin samun mai daga gare ta, a kuma samu kuli-kuli. Na fara makalar ne da bayanin cewa akwai hanya biyu ta yin hakan, wato tsohuwar hanya ta gargajiya wacce mafi yawancin ta da hannu ake tafiyar da ita, sai kuma […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (8)
Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (8)

A makon da ya gabata na yi makala a kan yadda za a sarrafa gyada, domin samun mai daga gare ta, a kuma samu kuli-kuli. Na fara makalar ne da bayanin cewa akwai hanya biyu ta yin hakan, wato tsohuwar hanya ta gargajiya wacce mafi yawancin ta da hannu ake tafiyar da ita, sai kuma hanyar zamani wacce mafi yawancin matakanta da injina ake tafiyar da su. Na yi bayanin yadda ake yin gargajiyar har ma na kai kusan karshenta, saboda haka zan karasa ta, sannan idan akwai sarari in fara bayani a kan yadda dan kasuwa zai shiga harkar yin man gyada da kuli-kuli na zamani.    
A makon na jiya na tsaya a kan yadda ake mayar da tunkuza ya zuwa man gyada da kuli-kuli, sai dai ban bambanta ire-iren kuli-kulin ba da kuma karbuwarsu a kasuwanni ba. Bayan na yi wannan bayani ne, idan da sarari nake da niyyar yin bayanin yadda dan kasuwa zai sarrafa gyada a zamanance domin kasuwannin gida da na kasashen waje.
kuli-kuli na kasancewa a siffa daban-daban, haka kuma yana kasancewa a dandano iri kamar uku: kuli-kuli maras gishiri, akwai kuli-kuli mai gishiri, akwai kuma kuli-kuli mai sukari. Idan kuma aka juya wajen siffa, kuli-kuli na iya kasancewa a dunkule kamar gayan fura, amma bai kai rabin gayan fura ba. Ya na kuma iya kasancewa tabe, wato a yi shi da fadi ba kuri, ko kuma a yi shi sirara da tsayi kamar siririn kara, da kuma masu da’ira wato masu kamar kawanya.
To, dukkanin kuli-kuli da ake yi ta hanyar tsari na gargajiya, ana yin sa ne domin amfanin jama’a, walau domin ci haka nan ko kuma a hada shi a cikin abinci. Mazauna Arewacin Najeriya sun san yadda ake cin garin kwaki da kuli-kuli da kuma yadda ake amfani da shi wajen yin kwadon tuwo da na ganyaye irin su zogale da yakuwa da rama da dai sauransu. Masu yin kwado na amfani da kuli-kuli da ya fi yawa a kasuwa, wato maras gishiri, wanda aka yi shi domin yin kwadon.
Shi kuwa mai gishiri ana yin sa ne domin ci, ana kuma soya shi ya soyu kwarai, ya yi tauri fiye da kuli-kulin kwado. Haka kuma dukkanin ire-iren kuli-kulin da na yi bayani a baya ana yin su ne domin ci, kuma ana yin su ne domin bukatar yara kanana, saboda haka ana soya su su soyu kwarai su yi tauri kamar margishi. An siffanta irin kuli-kulin da za a yi daga tunkuzar da aka tanada domin yin kuli-kulin. Misali, za a taba tunkuza ta yi fadi kafin a jefa ta a cikin mai a soya, daga wannan ake samun taben kuli-kuli. Haka kuma idan ana bukatar kuli-kuli mai siffar kawanya ko zobe, duk za a siffanta su ne tun daga tunkuza a zuba a ruwan mai da ke kan wuta a soya.
Shi kuwa dandanon kuli-kuli yana bambanta ne tun daga tunkuza. Wanda zai yi kuli-kulin kwado, ba zai sa gishiri a cikin tunkuzar yin wannan irin kuli-kuli ba, kuma ba za a bar shi ya dade a kan wuta kamar kuli-kulin ci ba. Shi kuwa margishi za a saka masa gishiri daidai gwargwadon iko tun daga tunkuza, haka zalika dukkanin launin kuli-kulin da za a yi da gishiri. Sannan kuma kamar yadda ake saka wa kuli-kuli gishiri, haka ma ake saka masa sukari. kuli-kuli mai sukari na daukar dukkanin siffofin da na lissafa a baya. A mafi yawancin lokuta za ka ga masu sayar da kuli-kulin ci na dauke da kuli-kuli mai gishiri da mai sukari domin zaben masu cin kowannensu.
Zan tattauna girman kasuwar kuli a kasar nan da ma yadda dan kasuwa zai iya fadada ta a cikin kasar nan da kuma yadda za a iya fita da shi ya zuwa kasashen ketare. Zan kuma tattauna yadda ake sarrafa gyada a zamanance, a karami da babban matsayi, domin fitar da manta da kuli-kuli, duk wannan zan yi in Allah Ya kai mu makon gobe.