Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (9)
A wannan makon zan tattauna girman kasuwar kuli-kuli a kasar nan da ma yadda dan kasuwa zai iya fadada ta a cikin kasar nan da kuma yadda za a iya fita da shi ya zuwa kasashen ketare. Idan mai karatu na tafe biye da ni, zai iya tunawa cewa a makon da ya gabata na […]
A wannan makon zan tattauna girman kasuwar kuli-kuli a kasar nan da ma yadda dan kasuwa zai iya fadada ta a cikin kasar nan da kuma yadda za a iya fita da shi ya zuwa kasashen ketare. Idan mai karatu na tafe biye da ni, zai iya tunawa cewa a makon da ya gabata na yi makala a wannan filin a kan yadda za a yi kuli-kuli iri-iri daga gyada ta hanyar gargajiya domin ci. Da farko na yi bayanin irin launikan abinci da za a iya hadawa da kuli-kuli, da kuma yadda kuli-kuli masu kama da dandano daban-daban ke da farin jini wurin yara. Za ka ga kuli-kuli a makarantu da sauran wurare da yara ke ziyarta, har ma da tashoshin mota da ma gefen tituna inda motoci ke jinkirtawa kafin su wuce.
kuli-kuli na daukar dogon lokaci, fiye da shekara, kafin ya lalace saboda soya shi da ake yi. Kuma leda da ake zuba shi a ciki na kara inganta rayuwar kuli-kulin ya zuwa lokacin amfani da shi. Wannan kasuwa ta kuli-kuli ta mamaye kasarnan daga Arewaci ya zuwa Kudancin kasar nan.
dan kasuwa na iya yin kuli-kulin ci da yawa, wanda shi ya fi kasuwa a gargajiyence. Yin kuli-kulin da yawa shi ne kara yawan gyadar da zai sarrafa da kuma rubanya dukkanin matakan yin kuli-kulin daidai gwargwadon iko, kamar yadda na yi bayani a makalun baya.
Sannan kuma zi iya adana kuli-kulinsa a mazubi na musamman domin kasuwannin gida da na waje. dan kasuwa zai lura da habakar da manyan shagunan kasuwanci (ko supermarket) suka samu a shekarun nan. Idan dan kasuwa ya waiwaya a cikin makalun da na yi a baya a kan adana kayayyakin abinci a mazubai domin kasuwa, za a ga dabarun yin haka da kuma ka’idojin da ake bukatar cikawa domin yin hakan.
dan kasuwa zai buga sunan kuli-kulinsa da na kamfaninsa da adireshin inda yake a wannan mazubi, zai kuma sa lambar amincewar Hukumar NAFDAC. A makalun baya na yi bayanin ka’idojin da za a cika kafin samun wannan lambar. Ita wannan lamba za ta ba wannan hajja ta dan kasuwa karbuwa a kasuwa, cewa wani abinci ne mai lafiya da hukuma ta yarda da shi.
Idan dan kasuwa ya cin ma fadada masana’antarsa ta yin kuli-kulin ci, ya kuma samu lambar NAFDAC, abin yi na gaba shi ne fadada kasuwarsa. dan kasuwa zai yi haka ne yayin da ya fara yin kuli-kulin, a lokacin kadarar ta shiga kasuwa, kada a ji labarinta a je kasuwa babu ita. Akwai hanyoyin fadada kasuwa da dama da na taba tattaunawa a makalun baya. daya daga cikin wadannan da za ta taimaka wa dan kasuwa kwarai da gaske a wannan yanayin, ita ce ta gabatar da hajarsa a kasuwa kai tsaye. dan kasuwa zai debi samfurin kuli-kulinsa ya kai irin wadannan manyan shagunan ya tallata musu shi. Zai ba wadannan shaguna kuli-kulin nasa a kan farashi mai sauki, kasa da farashin da ya yanke wa kowacce jikar kuli-kulin nasa, domin su ma su sami riba daga cikin harkar.
dan kasuwa zai yi mamakin da na ba shi shawararar kai kuli-kulinsa wadannan manyan shaguna, ban nemi ya fara da kananan shaguna ba. Abin da ya sa, wadannan shaguna su ne shagunan da masu kudin sayen kayayyaki ke zuwa da kudi suna neman abin da za su saya, sabanin kananan shaguna da masu halartarsu ke zuwa niyyar sayen abu daya, su saya su wuce. Kuma masu halartar manyan shaguna na yawo a cikinsa har su ga wasu abubuwa da ba su san da su ba, su kuma saya. A irin wannan zagayawa da masu ciniki suke yi a irin wadannan manyan shaguna za su ga kuli-kulin su saya. Idan kuma kuli-kulin dan kasuwa ya samu karbuwa a manyan shaguna to likkafarsa za ta daga a kananan shaguna, a rika nemansa ana saye.
Idan Allah Ya kai mu mako na gaba zan tattauna sauran hanyoyin da dan kasuwa zai bunkasa kasuwar kuli-kulinsa a kasuwannin gida da na kasashen ketare da kuma yadda ake sarrafa gyada a zamanance, a karami da babban matsayi, domin fitar da manta da kuli-kuli.