Sarrafa Albarkatun Gona: Man Kade (Man kadanya) 2
A makon jiya na gabatar da wannan makala sarrafa man kade a matayin daya daga cikin albarkatun gona da dan kasuwa zai iya sarrafawa domin cin kasuwannin gida da na kasashen ketare. A cikin makalar na lissafa dimbin amfanin da man kade ke yi wa jama’ar kasar nan. Wannan ya nuna karbuwar man a kasuwar […]
A makon jiya na gabatar da wannan makala sarrafa man kade a matayin daya daga cikin albarkatun gona da dan kasuwa zai iya sarrafawa domin cin kasuwannin gida da na kasashen ketare. A cikin makalar na lissafa dimbin amfanin da man kade ke yi wa jama’ar kasar nan. Wannan ya nuna karbuwar man a kasuwar kasar nan a gargajiyance. Na kuma fadakar da dan kasuwa game da yadda man kade ke samuwa da kuma jihohin kasar nan da ake iya samunsa. A wannan makon ne, kamar yadda na yi alkawari a makon baya, zan duba kabbuwar man kade a masana’antun Najeriya da na kasashen duniya da kuma matsayin Najeriya wajen wadata shi a kasuwannin duniya, da kuma yadda dan kasuwa zai sarrafa shi ya fitar da shi ya kuma amfana da shi a wadannan kasuwanni na duniya.
Masana’antun gida da na waje na sarrafa man kade su yi abinci da magunguna da mayikan shafawa kamar yadda masu amfani da man a gargajiyance ke yi. Misali, masana’antu na sarrafa man kade wajen yin abinci kamar man-bota (ko magirine da Turanci) da cakulan (chaculate) a madadin koko (cocoa) da nau’in burodi daban-daban. Suna kuma yin mayikan shafawa da sabulai iri-iri, kama daga na magani ya zuwa na kwalliya.
Masu sayen man kade daga Najeriya da ke kasashen Birtaniya da Amurka sun hakikance cewa man kaden da ke fitowa daga kasar nan ya fi na kowace kasa sinadiran kare jiki daga cututtuka da kuma warkar da lalurai. Saboda haka masana’antu a wadannan kasashe ke amfani da man kaden da ya fito daga Najeriya wajen yin man shafe-shafe iri-iri na kwalliya da na magunguna da man goge baki (toothpaste) da turare iri-iri. Su ma kasashen Nezaland da Faransa na cikin kasashen Turai da ke sayen man kade daga Najeriya domin sarrafa shi a masana’antunsu domin wannan bukata. kasashen Kwaddebuwa da Ghana da Togo na biye da Najeriya wajen wadata duniya da man kade.
Man kade na da babbar kasuwa mai fadi a duniya. Nahiyar Turai kadai na sayen fiye da tan 2000 na man kade, sannan kuma Amurka kanta na sayen fiye da tan 800 na man kade daga Najeriya. Irin bukatun da na lissafa a baya na dada sa mutane a duniya sanin man kade da karin neman kayayyakin da ake yi daga gare shi. Haka su ma kamfanonin da ke sarrafa shi su yi wadannan kayayyaki ke kara bukatarsa. Wannan ya sa kasuwar man kade ke bunkasa kullum a cikin duniya.
Kodayake yanzu an fara noma itacen kadanya a wadansu wurare a arewacin Najeriya domin samun man kade, amma mafi yawancin man da ake samu ana samunsa ne daga gonakin da ake samun itaciya daya ko biyu ko ma uku. Yawanci masu gonaki a arewacin Najeriya na shuka itaciyar kadanya mafi yawancin lokaci saboda inuwarta ko ‘ya’yanta ne domin abin marmari, wanda daga kwallayen ‘ya‘yan nata ne ake samun man make. Wadansu manoman ma na shuka itaciyar ne domin kwatance, ko kuma su shuka ta a kan iyakokin gona a matsayin alama.
Saboda haka dan kasuwa ba zai iya samun tarin wadannan kwallaye (kwara) da yawa a wuri daya ba domin ya saya ya sarrafa. Matan karkara ne da yara ke bi su tattara kwara. Wadansu masu tara kwara na busar da su su sayar wa masu yin man kade, ko kuma su sayar wa wadanda za su gyara su su sayar wa masana’antun gida ko su fitar da su ya zuwa kasashen ketare.
Idan Allah Ya kai mu mako na gaba zan yi bayanin yadda za a samu kwara da man kade da yadda za a sarrafa su domin sayar wa masana’antun gida da na waje.