Sarrafa Albarkatun Gona: Man Kade (Man kadanya) 3

A wannan makon ne zan yi wa dan kasuwa bayanin yadda zai  samu kwarar kadanya da man kade da yadda zai sarrafa su domin sayar wa masana’antun gida da na waje. Idan mai karatu na biye da ni zai iya tunawa cewa wannan ne kashi na uku na wannan makala, wacce na fara a makon […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Man Kade (Man kadanya) 3
Sarrafa Albarkatun Gona: Man Kade (Man kadanya) 3

A wannan makon ne zan yi wa dan kasuwa bayanin yadda zai  samu kwarar kadanya da man kade da yadda zai sarrafa su domin sayar wa masana’antun gida da na waje. Idan mai karatu na biye da ni zai iya tunawa cewa wannan ne kashi na uku na wannan makala, wacce na fara a makon shekaranjiya inda na gabatar da ita na kuma lissafa dimbin amfanin da man kade ke yi wa jama’ar kasar nan. Wannan ya nuna karbuwar man a kasuwar kasar nan a gargajiyance. Na kuma fadakar da dan kasuwa game da yadda man kade ke samuwa da kuma jihohin kasar nan da ake iya samunsa.
    A makon jiya kuma na duba karbuwar man kade a masana’antun Najeriya da na kasashen duniya da kuma matsayin Najeriya wajen wadata shi a kasuwannin na duniya. Na kuma fadi abubuwan da masana’antu ke yi da wannan mai da kuma kasashen da ke bukatarsa, musamman ma wadanda ke sayen man daga Najeriya.
   Yara da mata na tara kwarar kadanya a jihohin da ake samunta, ta bin wuraren da ake cin ‘ya’yan kadanya da kuma gonaki, wadansu lokutan ma dazuzzukan da ake samun itacen kadanya. ‘Ya’yan kadanya na samuwa a tsakiyar damina, wato daga watan Yuli zuwa na Agusta. Kuma kamar sauran ‘ya’yan itace da ake samu a arewacin Najeriya, kamar  su mangwaro da faru, ita ma kadanya ba ta da dogon zamani, tana gushewa a cikin karamin lokaci. Saboda haka, idan mai ita bai debe ‘ya’yanta a gonarsa ba za su zube su rube a cikin karamin lokaci. Haka kuma kadanyar da ta fito a jeji za ta zubar da ‘ya‘yanta, shi ya sa masu tsintar kwara ke samun wadatuwar ta a kusa da itacen kadanyar.
    Wadanda suka tsinci wadannan kwallaye suka tara na sayar wa dillalai da masu amfani da su kai tsaye, ko kuma su shanya su bushe, su zuba su a buhuna domin sayarwa ko sarrafawa a lokutan gaba. kwarar kadanya ta fi araha a wuraren da ta fi saukin samuwa, kamar jihohin da ke tsakiyar Najeriya da kuma jihohin Kudu da ke makwabtakar jihohin na tsakiya, fiye da jihohin Arewa maso Yamma da na Arewa maso Gabas. Shawara ga dan kasuwa a nan ita ce, yana da kyau ya nazarci kasuwar  kwara a duk shiyyar da ya je sayenta don samun kyakkyawan farashi. Mahimmancin yin haka shi ne, ana samun kwara a mazubai daban-daban, babu wani tsayyan mudu, saboda haka idan dan kasuwa ya san kima to zai iya sayen ko da wacce aka zuba a buhuna ce a farashi mai rangwame.   
    dan kasuwa da zai sarrafa kwarar man kadanya a gargajiyance, zai wanke ta ya tafasa ta a cikin manyan mazubai.  Zai sauke kwarar ya baza ta ta bushe. Yin haka zai ba shi damar fasa kwarar a cikin sauki ya fitar da ‘ya’yan da ke ciki. Wadannan ‘ya’yan ne kuma zai sake tafasawa su yi baki idan sun tafasa, ya yi ta juya su kamar yadda ake juya tunkuzar gyada har sai sun yi kauri kamar kulikuli, sun daskare. dan kasuwa zai mayar da wannan tunkuza ta ‘ya’yan kadanya kan wuta ya sake tafasawa har sai ta yi fara ta ba shi man kade.
    Akwai sabuwar hanya ta yin man kade da injin nika. Ana tafasa kwarar  ta huce a shanya ta, ta bushe a fasa a cire kwallon kamar yadda ake yi a gargajiyance. Busassun kwallayen ne ake nikawa a inji, inda za su zama tamkar bakar tunkuza. Za a cigaba da juya wannan bakar tunkuza har sai ta yi fari, sannan a mayar da ita kan wuta a dafa ta bayar da man kade idan an sauke ta huce.
    Zan yi bayanin sayar da kwarar man kade da man kaden kansa ga kamfanoninmu na gida da na waje, da kuma irin ribar da ke tattare da yin hakan, idan Allah Ya kai mu makon gobe.