Sarrafa Albarkatun Gona: Man Kade (Man kadanya) 4

A makon jiya na yi alkawarin zan yi bayanin sayar da kwarar man kade da man kaden kansa ga kamfanoninmu na gida da na waje a wannan makon, da kuma irin ribar da ke tattare da yin hakan. A kuma wannan makon ne zan kammala wannan makala ta sarrafa man kade domin sayarwa a kasuwanninmu […]

Sarrafa Albarkatun Gona: Man Kade (Man kadanya) 4
Sarrafa Albarkatun Gona: Man Kade (Man kadanya) 4

A makon jiya na yi alkawarin zan yi bayanin sayar da kwarar man kade da man kaden kansa ga kamfanoninmu na gida da na waje a wannan makon, da kuma irin ribar da ke tattare da yin hakan. A kuma wannan makon ne zan kammala wannan makala ta sarrafa man kade domin sayarwa a kasuwanninmu na gida da na kasashen ketare.
Idan ba a manta ba na yi shimfidar wannan makala makonni uku da suka gabata, inda na lasafta amfanin man kade da wuraren da ake iya samunsa a jihohin Najeriya, da kuma zurfin kasuwarsa a cikin kasar nan da kasashen waje. A makon shekara jiya kuma na duba karbuwar man kade a masana’antun Najeriya da na kasashen duniya da kuma matsayin Najeriya wajen wadata shi a kasuwannin duniya. Na kuma fadi abubuwan da masana’antu ke yi da wannan mai da kuma kasashen da ke bukatar sa, musamman ma wadanda ke sayen man daga Najeriya.
 Kamar yadda na yi bayani a makon jiya, dan kasuwa zai iya sayar da kwarar kadanya ko kuma man kade kansa ga kamfanonin da ke sarrafa su, a ciki da wajen kasar nan. Wata fadakarwar da zan yi wa dan kasuwar da zai yi wannan harka ita ce, akwai ka‘idar bayanin da zai makala a kan kowane mazubi da ke nunin abin da ke cikin mazubin da giredin man da kuma tsarkin man daga sinadaran da ka iya bata shi. Man kadai na samuwa a giredi hudu, daidai da kyansa; wato ‘A’ da ‘B’ da ‘C’da ‘D’. Wannan awo na tantance kyan man tare da irin rashin gurbatarsa daga wadansu sinadarai. Za a iya tantance matsayi ko giredin man kade a dakunan gwaji (produce laboratory) a ma’aikatun gona da na kasuwanci da ke jihohi. An fi samun giredin man kade matsakai ci a Najeriya, wato giredin ‘C’.  
dan kasuwa zai yi safarar man kade da mazubai kala uku, kamar haka:
1.   Rumbun (ko tanker da Turanci) man kade na musamman domin zuba shi, inda za a dumama shi idan ya isa kasashen ketare;
2. Dirarruka masu cin gallon 10 zuwa 50 da za a zuba man a rufe;
3. Kwalayen da aka yi wa shifidar leda da za a zuba man da ya huce ya fara daskarewa. Ana kuma iya zuba man kaden da ya huce a cikin buhunan da aka yi wa shimfidar leda a cikinsu.   
 dan kasuwa zai tabbatar da tsabtar wadannan mazuban kafin ya zuba man kaden. Zai wanke su, su bushe kafin ya yi amfani da su, sai idan ya sawo su daga masana’antu inda aka yi musu feshin kariya daga abubuwan da ka iya lalata abubuwa.
Idan mai karatu na biye da ni, zai iya tuna yadda na yi wa dan kasuwa bayanin yin man kade a kasidar makon da ya wuce. dan kasuwa zai nemi tsabtataccen kyalle ya tace man kaden da ya yi, bayan ya huce, kafin ya dura a cikin wadannan mazubai. Haka kuma zai yi idan sayen man kaden ya yi a kasuwa ko wurin masu yin sa. Ya fi kyau dan kasuwa ya sayi kwara ya yi mansa, idan kuma ya zama dole ya saya, to ya kasance ya san mai sosai, domin ya sayi mai kyau da abokan cinikinsa ba za su ki karba ba.
    Farashin kilo 50 na kyakkyawan man kade na kamawa daga Naira dubu dari da 80 da kakarsa,ya zuwa Naira dubu dari biyu da 50 a karshen kakarsa. Haka kuma ana sayar da shi a kasashen ketare daga Dalar Amurka  dubu da 800 (kimanin Naira dubu 320) ya zuwa Dala dubu uku (Naira dubu dari 450).
Allah Ya sa mu dace.