Sarrafa Albarkatun Gona: Ridi
A wannan makon zan yi bayani a kan yadda dan kasuwa zai shiga harkar saye da sayar da ridi a kasuwanninmu na gida da na waje. Ridi ba bako ba ne ga mazauna jihohin Arewa. A gargajiyence ana sarrafa kwayoyin ridi wajen yin kantu, abin da a wadansu shiyyoyin Arewa ake cewa ridi, inda wadansu […]
A wannan makon zan yi bayani a kan yadda dan kasuwa zai shiga harkar saye da sayar da ridi a kasuwanninmu na gida da na waje. Ridi ba bako ba ne ga mazauna jihohin Arewa. A gargajiyence ana sarrafa kwayoyin ridi wajen yin kantu, abin da a wadansu shiyyoyin Arewa ake cewa ridi, inda wadansu ke canja masa suna idan aka sarrafa shi; wato a irin wadannan wurare ridi shi ne tsabar ridin da ba a sarrafa ba, sai kuma a kira wacce aka sarrafa da wani sunan, inda kamar a Kano ake ce masa kantu. A sauran wurare kuwa ridi ba ya canja suna ko da an sarrafa shi ya zuwa wani launin abinci.
A matsayin abinci a kasar Hausa a kan samu ridi a soye da sikari ko da gishiri a darkare ko a yaska, wato a cikin tsabarsa da ake kullawa a cikin leda. Ana yin kunun ridi da kulikulin ridi da sauran kayan lashe-lashe. A kan kuma saka ridi a jikin biredi ko fanke iri-iri. Ana kuma yin miyar ridi ko kuma miyar ganyen sa.
Ana kuma sarrafa ridi a masana’antunmu na gida da na waje wajen yin kayayyakin abinci da na magunguna da kuma tatsar man ridin domin samun man girki, wanda ya fi kowane man girki da ake samu a Najeriya farashi, kama daga man gyada ya zuwa man ja da man angurya. Ana amfani da ridi wajen yin burodi da biskit da man bota na shafawa a burodi da kuma sinadaran hada abinci masu inganta cimaka wajen dandano da kamshi, musamman ma a abincin kasashen gabas irin su Indiya da Japan da makamantansu.
Ana kuma sarrafa ridi wajen yin magunguna irin na alsa (ko ulcer da Turanci) da kuna. Masa’antun kuma na amfani da ridi wajen yin sabulai da kayan shafe-shafe da fenti da maganin kwari da abinci dabbobi. Wannan ya nuna fadin da kasuwar ridi ta ke da shi, saboda irin bukatar da ake da ita ta ridi a ciki da wajen kasar nan. Wannan kuma zai ba dan kasuwa hasken mahimmancin wannan hatsi a kasuwance.
Najeriya ita ce kasa ta biyar a sahun manya kasashe goma na duniya da ke noma ridi, inda take noma kimanin tan dubu 160; tana kuma biye da kasar Sin (China) da Indiya da Mayanmar da Sudan da Uganda a wannan sahun. Ana samun ridi a jihohin Kano da na Jigawa da Yobe da Barno da Bauci da Binuwai da Nasarawa da Babban birnin Tarayya, Abuja.
Najeriya ce kuma kasa ta shida a sahun manyan kasashe goma masu sayar da riki a duniya, inda take bin sahun kasashe irin su Indiya da Sudan da kasar Sin da Itofiya,inda take kai kimanin tan dubu 45 kasuwa. kasashe goma da suka fi sayen ridi a duniya sun hada da Japan da Masar da Tarayyar Turai (European Union) da Koriya da Amurka da Sin da Siriya da Turkiyya da kasashen Larabawa da Isra’ila. Kuma ridin Najeriya ya fi samun kasuwa a Tarayyar Turai da Amurka da Japan.
Idan Allah Ya kai mu makon gobe zan yi bayanin yadda dan kasuwa zai samu ridi ya sarrafa shi domin sayar wa masana’antunmu na gida da na kasashen ketare.